Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, Gwamnatinsa na kan yin duk mai yiwuwa wajen magance hauhawar farashin kayan masarufi a daukacin fadin Nijeriya.
Buhari ya bayyana hakan ne a Abuja a yayin bude taron ma’aikatun gwamnatin Tarayya karo na Uku dake yin nazari kan ayyukan da gwamnatin Buhari ta wanzar na kudurori 9.
Shugaban ya ce, muna kan yin dukkan mai yiwuwa domin ganin mun magance hauhawar farashin kayan masarufi a daukacin fadin kasar nan.
A bisa kididdigar da hukumar kididdiga ta kasa ta fitar NBS a kwanan nan, ta nuna cewa, hauhawar farashin kayan masarufi ya karu zuwa kashi 20.77 cikin 100 a cikin watan Satumba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp