Alamu sun nuna cewa akwai babbar munakisa da ke cikin batun tsige shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da wasu ‘yan majalisa suka yi yunkurin yi.
A cikin wannan makon, fadar shugaban kasa ta fito karara ta nuna cewa ba za ta taba bari a tsige Akpabio ba duk da irin alwashin da wasu ‘yan masalisan suka yi kan batun.
Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta shaida wa LEADERSHIP cewa shugaban kasa zai kare kujerar Akpabio yadda ya kamata bisa yunkurin tsige shi idan majalisar dattawa ta koma hutu a karshen wannan watan.
Majiyar ta ce fadar shugaban kasa za ta yi taka-tsan-tsan wajen tsige shugaban majalisar dattawa, domin lamarin na iya haifar da rudani wanda zai iya yaduwa har zuwa majalisar wakilai.
A cewar majiyar, duk da cewa fadar shugaban kasa ba ta ji dadin kalaman da Akpabio ya yi a baya-bayan nan, shugaban kasar na burin ci gaba da mukamin Akpabio ne domin a samu kwanciyar hankali, inda ta kara tabbatar da cewa babu hasashen canjin shugabanci a majalisar dattawan Nijeriya a halin yanzu.
Majiyar ta kuma ce fadar shugaban kasa ba za ta yi wasa ba har abokan hamayyar siyasa su yi amfani da wannan dama domin kwace shugabanci a zauren majalisa.
‘Yan majalisun da suka sha kaye da wadanda ba su sami shugabancin kwamiti masu gwabi ba sun yi ta korafe-korafe wanda ake ganin su ne suke ci gaba da ruruta wutar tsige shugaban majalisan.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa kalaman da Akpabio ya yi kan kudin hutun ‘yan majalisa ya sa wasu makarraban Shugaban Tinubu suka fara tunani na neman wanda zai maye gurbin Akpabio.
A karshen makon da ya gabata, LEADERSHIP ta kuma bayar da rahoto na musamman kan yunkurin tsige Akpabio da wasu fusatattun ‘yan majalisa suka yi.
Tuni dai wasu ‘yan majalisa guda biyu daga yankin arewa maso yamma suka jagorantaci wasu sanatoci tattaunawa na yunkurin shirye-shirye aiwatar da tsige shugaban majalisan dattawan.
Fasatattun sun yi zargin cewa shugaban majalisar dattawa ya samu wannan matsayin ne sakamakon goyon bayan shugaban kasa yanzu kuma sun lura cewa ba zai iya gudanar da aikinsa yadda ya kamata ba.
Sai dai shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yada labarai, Yemi Adaramodu, ya yi watsi da barazanar tsige shugaban majalisan. Ya ce wannan yunkurin ne mara tasiri, domin ‘yan majalisar dattawa kan kan su a hade yake.
Ana sa ran majalisan dattawan za ta dawo daga hutu ne a ranar 26 ga Satumba.
Lokacin da aka tuntubi wani dan majalisa wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “An sayar mana da ‘yancinmu ba tare da la’akari da irin nau’yn da ke kanmu ba. Babu wata alkibla da za a amsa daga wurinmu a matsayinmu na ‘yan majalisa.”
Dan majalisar ya ce, “Dangane da abin da ya shafi karamar majalisar, dole ne a fara komai daga fadar shugaban kasa, wanda daga can ne aka hada shugaban majalisar wakilai. Majalisa ta 10 ita ce mafi muni kamar yadda muke iya gani. Mun fi muni fiye da hadin kanmu, ba ma cin gajiyar kanmu a matsayin bangare majalisa masu yin dokoki, sai dai abin da bangaren zartarwa ke so shi ake aiwatarwa.
“Ba labari ne cewa babban mai taimaka wa shugaban kasa da mukarrabansa ne suka hada shugabannin kwamitoci tun daga fadar shugaban kasa, wanda suka danne wadanda ba su so ko wadanda suke ganin suna adawa da Abbas kan rashin ba su kwamitoci masu gwabi.
“Abin takaici ne matuka, domin a majalissar ta 2019, wasun mu sun yi musu tawaye. Ko Wase ya sauka daga layinsu, amma yanzu ga mu nan a jibge. Don haka idan wani abu ya faru da kujerar Akpabio, zai yi tasiri ga Abbas kuma babu wanda zai iya hana shi,” in ji shi.
…Akpabio Ya Shirya Labarin Tsige Shi Don Hada Fada Tsakanin Tinubu Da Sanatocin Arewa – Sanata Abbo
Dan majalisa mai wakiltar Adamawa ta arewa, Sanata Ishaku Abbo, ya bayyana cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ne da kansa ya shirya labarain tsige shi, domin ya kawo sabani tsakanin Tinubu da wasu sanatocin arewa.
Abbo ya kuma kara da cewa shugaban majalisar dattawa ne ya shirya wannan labari domin kawo rashin jituwa tsakanin shugaban kasa Tinubu da wasu ‘yan siyasar arewa.
An dai bayyana cewa Akpabio ya musanta zargin da ake yi masa wanda ya kawo maganar tsige shi. Ya siffanta wadannan rahotanni a matsayin mara tushe balle makama.
An samu rahotanni a kafafen yada labarai a ranar Asabar da ta gabata cewa, ana shirin tsige Akpabio daga shugabancin majalisar dattawa na 10 a lokacin da majalisar za ta koma hutu a ranar 26 ga Satumba, 2023.
Ya ce, “A yau na farka na iske jaridun Nijeriya sama da 10 duk suna dauke da labarin shirin tsige Sanata Akpabio da ‘yan majalisar dattawa daga arewacin Nijeriya ke shirin yi. Har da jaridar Whistler ta anbaci sunan Sanata Abdulaziz Yari da Sanata Aminu Tambuwal da Sanata Ogoshi Onawo da dai sauransu, a matsayin sanatoci da suka yi wannan yunkurin.”
Tun lokacin da Nijeriya ta dawo mulkin dimokuradiyya, tarihi ya nuna cewa zuwa yanzu shugabannin majalisar dattawa biyu ne kacal aka tsige daga mukamansu, yayin da aka tilastama guda daya ya rubuta murabus da kansa ba tare da nuna wata adawa ba.
Wadanda aka tsige sun hada da, Marigayi Sanata Ebans Enwerem da Sanata Chuba Okadigbo. Sannan kuma Sanata Adolfus Wabara ya yi murabus da kansa.