Mataimakin shugaban Babbar kungiyar dillalai masu sauke Doya da sayar da ita ta Nijeriya wadda ke da ofishinta Ababbar kasuwar sayar da Doya unguwar Mile 12 ta jihar Legas.
Alhaji Tijjani Dammasu Kudi Igabi ya ce, suna yin taro a duk Shekara domin gudanar da addu’o’i na musamman ga ‘yan kasuwa masu sana’ar doya da sauran ‘yan kasuwa masu zuwa Arewacin Nijeriya domin su siwo kaya su kawo jihar Legas domin sayar wa al’uma su ci gaba da sanaarsu ba tare da sun shiga wasu matsaloli ba.
Mataimakin ya yi wannan tsokaci ne a harabar ofishin kungiyar da ke jihar Legas ya ci gaba da cewar suna gudanar da wannan taro ne a daidai wannan lokaci da sabuwar doya ke fito wa a wuraren da ake nomata tare da murnar fitowar sabuwar doyar da fatan alheri ganin cewar an samu ci gaba a kasuwancinta a cikin wannan shekarar, ya kara da cewar a kan haka ne ya ummarci ‘yan kasuwar Musulmi da Kiristoci da su rika gudanar da irin wannan addu’ar a lokacin da suke gudanar da harkokin Ibadarsu Taron ya kunshi Hausawa da Yarabawa da Inyamurai da Tibi da Gara da sauran nau’in. kabilan Nijeriya.
Ya kara da cewar wajibi ne shuwagabannin kungiyar su kara nemo hanyoyi da za su taimaka wa kasuwar domin samun karin zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba mai ma’ana sannan ya ce a kan haka ne kwamitin Kasuwar ya canza dokokin. Dillacin Doya musamman ga dillalai masu rike kudin fatakensu da sunan sun ba da bashi ba za su yarda da irin wannan ba da sauran dokoki makamantan wannan.
Karshe ya yaba wa Gwamnatin Janaral Mahmadu Buhari a kokarinsa na kawo karshen fitintinu da Nijeriya ke fama da su domin al’umma su ci gaba da zama lafiya.