Wata Kotun Majistare da ke Normansland a Kano ta yanke hukunci ga wasu mutane biyu bisa laifin haɗa baki da kuma sare bishiya ba bisa izini ba, wanda ya saba dokokin kare muhalli na jihar.
A cewar wata sanarwa daga Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano, kotu ta same su Salihu Mukhtar da wani abokinsa da laifin sare itace ba tare da izini ba a kan titin Jigawa da ke unguwar Nasarawa GRA.
- Bayan Shekaru 7 Yana Ɓoye, NDLEA Ta Cafke Babban Dillalin Ƙwayoyi
- Ƴansanda Sun Kama Ɗalibai 11 Kan Kisan Wasu Ɗalibai 2 A Kano
Lauyan gwamnati, Barrister Bahijjah Aliyu, ta gabatar da hujjoji da suka tabbatar da cewa waɗanda ake tuhuma sun haɗa baki wajen aikata laifin, wanda ya saɓawa dokokin laifuka da na dazuka na jihar Kano.
Mai shari’a Auwalu Yusuf ya yanke hukunci da cewa: “Domin haɗa baki, za su yi wata uku a gidan yari ko su biya tarar Naira dubu ashirin kowanne. Kan laifin sare itace ba bisa ƙa’ida ba, za su yi wata shida a gidan yari ko su biya tarar Naira dubu hamsin kowanne.”
A wani ɓangare, Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar Kano, Dr. Dahiru Hashim, ya jaddada cewa gwamnati ba za ta lamunci sare dazuka ba tare da izini ba, yana mai roƙon jama’a da su riƙa kai rahoton irin wadannan laifuka. Ya ce: “Itatuwa ba ado ba ne kawai, suna da muhimmanci ga iskar da muke shaƙa, yanayin da muke rayuwa a ciki, da makomar da muke ƙoƙarin gina wa.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp