Gwamnatin Jihar Yobe, ta sanar da cewa mutum tara sun mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a kananan hukumomi biyar na jihar.
Kwamishinan Lafiya da Harkokin Jin Dadin Jama’a na jihar, Muhammad Gana ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Damaturu, babban birnin jihar.
- Wakili: Kasar Sin Tana Adawa Da Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kan Fararen Hula
- Xi Jinping: Inganta Gina Dunkulewar Kabilun Kasar Sin Baki Daya
Ya ce an tabbatar da barkewar cutar a yankunan Machina, Nangere, Gujba, Nguru, da Fune.
A ranar 25 ga watan Satumba, an samu rahoton cewa mutane 132 sun kamu da cutar, inda aka sallami mutum 112 bayan an ba su magani.
Gana, ya bayyana cewa ruwan sama mai yawa da ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar ya haifar da karuwar cutar amai da gudawa, wanda hakan ya taimaka wajen bazuwar cutar kwalara.
Ya yi kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da ba da goyon baya ga kokarin gwamnati don shawo kan lamarin.
Gwamnatin jihar ta ce tana aiki tare da sauran hukumomi domin kara inganta matakan shawo kan cutar da kare lafiyar al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp