Rundunar ‘yan sandan Jihar Ekiti ta gurfanar da wasu mutane 17 da ake zargi da aikata laifuka a jihar tare da kwato wasu makamai a hannunus.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ogundare Dare, ya ce rundunar ta kama mutanen da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.
- Yanzu-yanzu: Tsohon gwamnan Anambra, Mbadinuju Ya Rasu
- El-Rufai Ya Jinjina Wa Sojoji Kan Kashe Kasurgumin Dan Bindiga, Danwasa A Kaduna
Da ta ke gabatar da wadanda ake zargin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Sunday Abutu, ta ce rundunar ‘yan sandan ta RRS a ranar 6 ga watan Afrilu, ta hanyar kai farmakin daji, sun kama wani Augustine Agboobo, Adeniyi Olamilekan, Williams Ukeuima Friday da Ademoh Gabriel, a cikin dajin da ke kusa da yankin gonakin Igede.
“A yayin da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa cewa su ‘yan kungiyar masu garkuwa da mutane ne da suka gudanar da ayyukan garkuwa da mutane a jihar Ekiti ciki har da sace Ajibade Adeleke a gonar Igede da kuma karbar kudin fansa wasu”.
Abutu ta kara da cewa rundunar ta kama wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne tare da hadin gwiwar wasu al’umma a Oke-Ureje da ke Ado-Ekiti a ranar 4 ga watan Afrilu da misalin karfe 22:00 sannan ta kama Saliu Oyebamiji da Ajisefe Mayowa.
Haka kuma, an kama wani fitaccen dan fashi da makami mai suna Jimoh Gani a ranar 4 ga watan Afrilu, bisa laifin yin fashi da makami da yi wa wata dalibar Jami’a fyade a Ikere-Ekiti.
“Lokacin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.”
Rundunar ta kwato kayayyaki daban-daban da suka hada da bindigar gida daya, bindigar maharba guda daya da buhun tabar wiwi da sauransu.
Rundunar ‘yan sandan ta yi kira ga daukacin ‘yan kasar nan da su kula da harkokin tsaro tare da kai rahoton duk wani abu da ya faru a yankinsu ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.