Kwamishinan lafiya na Jihar Bauchi Dakta Adamu Sambo, ya ce an samu barkewar cutar Sankarau wato meningitis (CSM) har guda shida a fadin jihar.
Kwamishinan ya ba da tabbacin ne a lokacin da aka masa tambaya dangane da barkewar cutar Sankarau a jihar da ke makwabtaka da Bauchi wato jihar Yobe.
- “Tsadar Kayan Gini Zai Haifar Da Karuwar Rugujewar Gine-gine”
- Shugaban Najeriya Ya Kaddamar Da Layin Dogo Da Kamfanin Sin Ya Gina A Legas
Ya ce’m: “Eh, muna da CSM. Mun samu guda 6 da aka tabbatar a sassa daban-daban na jihar.”
Sai dai kuma, gwamnatin jihar ta ba da tabbacin daukan matakan da suka dace wajen ganin ta dakile yaduwar cutar Sankarau a fadin jihar baki daya.
Matakan da gwamnatin ta fara dauka na magance yaduwar cutar sun fi karfi a arewacin jihar yankunan da suka hada iyaka da jihar Yobe wato Gamawa, Dambam, Zaki, Katagum da kuma karamar hukumar Itas/Gadau.
Wani ma’aikacin hukumar kula da lafiya a matakin farko na jihar Bauchi da ya roki a sakaye sunansa, ya tabbatar da cewa akwai barkewar cutar a wasu kananan hukumomin da ke arewacin jihar sai dai na shi ne ke da ikon shelanta wa duniya hakan ba.