Daya daga cikin fitattun Jaruman fina-finan Hausa ta Kannywood, kana mawakiya a fannin Siyasa da kuma cikin masana’antar Kannywood. Jarumar da ta shafe shekaru goma sha hudu tana taka rawa a fim da kuma waka, wato SUWAIBA ABUBAKAR wadda aka fi sani da MAKAUNIYA. Ta bayyana wa masu karatu manyan Jaruman da suka zamo allon kwaikwayonta cikin masana’antar ta shirya fina-finan Hausa, wadanda take jin da ma ta zama kamar su, kana ta bayyana irin nasarar da ta samu cikin masana’antar wanda ba kowa ke samu ba cikin jaruman, har ma da wasu batutuwan masu yawa. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:
Ya sunan jarumar?
Sunana Suwaiba Abubakar wadda aka fi sani da Makauniya.
Me ya sa ake kiranki da Makauniya?
Sunan fim din dana fara yi ne.
Ko za ki fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
To ni dai an haife ni a Dutsinma dake Jihar Katsina, nayi karatun a Dutsinma iya sakandare, sannan kuma nayi aure duk a Dutsinma. Ba ni da yara kuma ba ni da aure a yanzu.
Kin ci gaba da karatu ko kuwa a wanne mataki kika tsaya?
A’a ban ci gaba ba, na tsaya ne a matakin sakandare.
Me ya ja hankalinki harhar kika fara fim?
Saboda ina da sha’awar harkar ne tun farko.
Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?
Eh! gaskiya ni ban fuskaci wani kalubale wajen shiga ba, ban sha wahalar shiga ba.
Toh ya batun iyaye fa lokacin da kika sanar musu cewar kina sha’awar shiga masana’antar, shin kin fuskancin wani kalubale daga gare su?
Eh! to da yake muna da fahimtar juna sosai, nasiha suka yi mun cewa na ji tsaron Allah Aduk inda nake, kuma suka bani amanar kaina.
Za ki kamar shekara nawa da fara fim?
Zan yi kamar shekara goma sha hudu 14 da fara fim.
Da wanne fim kika fara kuma wacce rawa kika taka cikin fim din?
Na fara da fim din ‘Awarwasa’, kuma ni ce Jarumar fim din. Na fito a ‘yar mai kudi, kuma mahaifiyata ta rasu matar babana tana gallaza min har na shiga bariki, daga karshe nayi aure kuma ina bin maza har na samu HIB.
Ya kika ji a lokacin da fim din ya fita, ganin kin fito a Bariki, kuma shi ne farkon farawarki, shin kin fuskanci wani kalubale daga wajen mutane kamar masu kallo ko ‘yan uwa, da sauransu?
Eh! to kin san ai dole ne wannan.
Kafin shigar ki fim wanne abu ne ya fara baki tsoro game da fim, wanda har kike jin gwara ki barshi?
Eh! to da yake lokacin gaskiya babu rashin tarbiyar sosai a masana’antar.
Kin yi fina-finai sun kai kamar guda nawa?
Za su kai kamar guda ashirin 20.
Ko za ki fada wa masu karatu kadan daga ciki?
Eh! akwai Awarwasa, Makauniya, Duniya, Labari, Rubutacciya, babban Gida, Zama da Kishiya, da sauransu.
Idan aka ce ki zabi guda wanda kika fi so, cikin finafinan da kika fito, wanne za ki dauka wanda ya zamo bakandamiyarki?
Zan dauki Makauniya, sabida da shi ne nayi suna kowa ya sanni.
Ko akwai wani kalubale da kika taba fuskanta cikin masana’antar bayan shigarki?
Eh! to kin san kowacce sana’a ai dole ne haka ta faru, akwai kalubale.
Wanne irin nasarori kika samu game da fim?
To Alhamdu lillah tun da na fara ban taba samun matsala da kowa ba har zuwa yau, wannan babbar nasara ce a gare ni.
Wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ki taba iya mantawa da shi ba a rayuwa?
Rashin mahaifina shi ne mafi girman al’amari cikin rayuwata.
Me kike son cimma game da fim?
Alhamdulillah na cinma duk abin da nake so a fim.
Ya kika dauki fim a wajenki?
Na dauki fim a wajena sana’a.
Bayan sana’ar fim da kike yi, shin kina wata sana’ar ne?
Eh! Ina waka da kuma kasuwacin sai da kayan kitchen da sauransu.
Yaushe kika fara waka, kuma me ya ja hankalinki har kika fara waka?
Na fara waka shekaru goma 10 da suka wuce, kuma dama ina da ra’ayi akan waka tun farko gaskiya.
Wacce waka kika fara, kuma ya karbuwar wakar ta kasance ga su masu sauraro?
Wakar wani fim ne na Zo Mu Leka, da ni da Sani Hassan.
Kin yi waka sun kai kamar guda nawa?
Suna da yawa gaskiya, amma na siyasa sun fi yawa.
Kamar wadanne kika yi a na siyasar?
Wakar Satomi da Masari da Uba Sani da Aminu Balele dan Arewa.
A cikin wakokinki wacce tafi fice aka fi sani?
E! wadda aka fi sani ita ce ta Satomi.
Ke kike rubuta waka da kanki ko wani ne yake rubuta miki?
Rubuta mun ake yi ina rerawa, wani lokacin kuma ina rubutawa.
Kamar da wanne lokaci kika fi jin dadin yin rubutu?
In zan rubuta waka da dare tafi dadi.
Me ya fi ba ki wuya a fanni waka da kuma fim?
Gaskiya babu.
Wace rawa kika fi yawan takawa a fim?
E! kowanne bangare ina iya kokarina.
Kafin ki fara fim wanne Jarumi ko Jaruma ce ke burge ki, wanda har kike ji dama ki zama kamar su?
Iyan Tama shi ne jarumina lokacin gaskiya,da Hajara Usman.
Ko kina da ubangida a masana’antar kannywood?
Eh! ina da ubangida shi ne Yahaya Baba Wulyam.
Wa ce ce babbar kawarki a Kannywood?
Ba ni da babbar kawa.
Ya alakarki take da sauran abokan aikinki?
Muna mutunta juna da kowa.
Yaushe kike sa ran kara yin aure, tunda aure lokaci ne?
Haka ne, ko yanzu Allah ya kawo mijin ina shirye in sha Allah.
Mutane na yi muku kallon masu furta wannan kalmar ta ko yanzu kuka sami miji za ku yi aure a iya baki kawai, ba wai har zuci ba, domin ko da kun samu mijin ba auren kuke yi ba, me za ki ce akan hakan?
Ta yiwu mutanen suna fahimtar abin da nasu kallon ne, amma aure in ya zo yinshi kawai ake yi indai mijin da gaske ya zo.
Ko akwai wanda kuka yi alkawarin aure da shi ko kuke tunanin yin hakan cikin masana’antar?
Ban taba soyayya da kowa ba bare muyi maganar aure.
Idan wani ya ce yana son aurenki cikin masana’antar shin za ki amince ko ba ki da ra’ayin hakan?
Eh! Mana sosai ma zan amince.
Wanne irin abinci kika fi so?
Shinkafa da Miya.
Kayan sawa fa?
Na fi son Doguwar Riga.
Mene ne burinki na gaba game da fim da kuma waka?
In gama da su Lafiya.
Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shiga masana’antar Kannywood har ma da wadanda ke ciki?
Su yi kokari su rike ta sana’a, kuma su ji tsoron Allah.
Ko akwai wani kira da za ki ga gwamnati game da harkar fim?
Eh! kirana ga gwamnati shi ne da ta sa hannu wajen tallafawa masana’antar dan ci gabanta.
Me za ki ce ga masoyanki da masu kallon finafinanki?
Ina yi wa duk masoyina fatan alkairi a koda yaushe.
Me za ki ce ga makaranta shafin Rumbun Nishadi?
Ina yi musu fatan alkhairi su ci gaba da kasancewa tare da wannan shafin.
Me za ki ce da ita kanta Jaridar LEADERSHIP Hausa?
Ina yi wa jaridar Leadership addu’ar fatan alkairi.