Connect with us

LABARAI

Na Fito Takarar Gwamna Ne Don Gazawar Gwamnatin Ganduje  -Akibubello

Published

on

Akibu Ibrahim Bello na daya daga cikin ‘yan siyasa da suka fito domin neman takarar kujerar Gwamnan Kano, amma shi takarar tasa yana yi ne a karkashin inuwar jam’iyyar APC, wacce ita take mulkin jihar.

A wannan tattaunawar da wakilimmu a Kano, Ibrahim Muhammad ya yi da shi, Akibu ya bayyana dalilinsa na neman kujerar Gwamnan. Ga dai ya dda hirar ta kasance.

Kana daya daga cikin wanda ake ganin fuskokinsu a neman takarar Gwamnan jihar Kano a Jam’iyyar APC. Ko wane dalili ne ya kawo haka, ganin cewa Gwamnatin da APC ta kafa ne ke mulki?

Kamar yadda ka fada, sunan Akibu Ibrahim Bello, ni dan jam’iyyar APC ne, tun a baya ma ina cikin APP, ANPP, CPC zuwa APC. Kuma ni dan siyasa ne kamar yadda kowa ya riga ya sani. Kuma wannan jam’iyya ce ta “merger.”

Kamar yadda nake fada cewar ita hadaka ce ta wasu ‘yan siyasa, wacce ta hada jam’iyyu da wasu daga cikin PDP, wanda a kwanaki sun fita sun koma inda suka fito.

Amma  duba da cewa irin abubuwan da ke fitowa a Gwamnatin jihar Kano na rashi dadi, ba dan komai ba, kowa yana kallon abin da ke faruwa, duk da jam’iyyar mu ce, amma sai mu ce wanda ke jagorantarta a matsayinsa na shugaba da masu goya masa baya sun san cewa an gaza, wanda mu muna ganin kamar an zuba mana kasa a idanunmu ne.

Saboda shi Buhari ya yi iya kokarinsa dan ya taimaki al’umma ya ga cewa kasar nan ta hau kan layi yadda ya kamata, amma duba da yadda Kano ta zama a yanzu akwai bukatar a samu canji, ba dan komai ba, saboda wanda ke jagorantar al’amarin da mukarrabansa ya kamata su dubi Allah su sani cewa akwai abubuwa da dama da aka gaza cikin wannan al’amari.

Wannan ce ta sa saboda kaunarmu ga jam’iyyar da son ci gaba muka ga ya kamata, tunda mu ‘yan siyasa ne mu fito mu bada gudummawa domin kar APC ta fadi a zabe mai zuwa. Wannan shi ne dalili na farko.

Sannan na biyu. Duk wani dan siyasa da ke son taimaka wa al’umma, don ta wannan ne  za ka iya bada gudummawar  da za ta amfani al’ummar da kake kishinta  kake fatan ta hau kan layi.

Saboda haka wannan shi ya sa na fito takara, saboda al’umma na godon fatan Allah ya sa a sami wanda  zai zo ya taimaka.

Kuma kiraye-kiraye daga talakawa da mutane masu kishin al’umma da addini ya sa muka ga ya kamata mu fito wannan takara da muke tsakani da Allah. Kuma muna fata Allah ya kai mu ga nasara.

 

Kana ganin cewa a wannan takara taka, za a iya yi maka adalci wajen zaben fidda gwani?

Ai babu zancen wannan. In dama a ce ana adalcin, to ai babu zancen fitowa ta takara. Zamu iya yi masu fatan alhairi, Allah ya kai shi ga nasara, amma wannan ba wani abu ba ne.

Abin da mutum ya kamata ya rika dubawa shi ne, mulki a hannun Allah yake, ba a hannun wani ba, duk inda za ka kai ga cukwikwiye wani abu, to in Allah ya yarda a cikin wannan cukwikwiyewar da yake, nan cunarsa zata fada, kaima ka fadi badan komai ba saboda shi zalunci ba ya kaiwa ko’ina.

Saboda da ikon Allah muna da yakinin Allah zai fitar da mu daga kunci da tasku da tunanin cewa in Allah ya kawomu muna da shugaba wanda yake so ya ga mutane sun sarara daga halin da aka samu kai a baya, amma wasu kadan daga cikin mutane sai cukwikwiye wannan suke yi.

Don haka Allah yana sa ne da su, ba zai kyalesu ba, mulki a hannunsa yake zai canzasu lokacin da ya ga ya dace da ikon Allah.

 

Wane irin goyon baya al’ummar Kano ke baiwa wannan takara taka?

Mutanen Kano da su kansu wadanda suke tare da Gwamnati a yanzu suna bada goyon bayansu, sai dai dan adam ba kowa ke da karfin zuciya na fitowa fili ya nuna zai taimaka akan wannan al’amari ba. Saboda mutum yana ganin zai sami wani abu, wani na bukatar  dan mulkin da yake kai, wani ‘yan kwangiloli da makamantansu ba za su bari wani ya fito fili ya bayyana ba, amma a zuci inka kebe da shi zai ce muna da bukatar canza wannan al’amari daga halin da  ake ciki izuwa wani halin.

Zuwa yanzu ka shirya shiga zaben fitar da gwani da jam’iyyarku ta ce ‘yar tinke za a yi?

Eh! Gaskiya ne na shirya, ko ‘yar tinke za a yi ko ‘yar wacce za a yi, duk abin da za a yi na shirya, saboda wannan abu tunda a wurin Allah ake nema, da su al’umma da suke da kishin abin.

Don haka ina ganin na shirya zan kuma yi iyaka kokarina saboda ba takara ce ta wani ba, takara ce ta al’umma, ba wanda ya sa ni, ba wanda ya tsayar da ni, ba wani abu makamancin wannan. Babban burimmu mu hadu gaba daya da al’ummar da ke cikin wannan tasku mu kai ga nasara.

 

Ana kukan cewa APC ta tsawwala kudin sayen fom na takara. A matsayinka na dan takara yaya kake duban wannan?

Gaskiya ne wannan al’amari ne na ban mamaki, saboda PDP ta saida nata akan abin da bai wuce Naira Miliyan Shida ba, akwai wasu ma da suke saida kasa da haka, saboda suna ganin abu ne da suke bukatar al’umma, amma mu jam’iyyarmu ba mu san dalili ba. Amma  har yanzu mun tsaya mu gani.

Saboda abin da  ake yaki da rashawa da cin hanci da sauran nau’o’i na almundahana, wannan shi ne aka ce  ana yaki a APC.

Amma in har ana ganin talaka, wanda ba shi da wani abu a hannunsa, babban burinsa shi ne taimakawa wajen ci gaban al’umma, an sa musu kudi wanda suka fi karfin hankalinsa, to ina ganin wannan akwai wani abu da ake nufi.

A kasashe zai wahala a ce an sami wata kasa ta tsawwala kudin takara, amma a kasar nan a ce za a yi wannan a APC, wannan abin akwai abin da za a duba a ciki.

Muna biyayya ga jam’iyya, ba d on komai ba, mun yarda lallai akwai manufarta akan wannan lamari, muna nan muna jira ta dubi yadda al’amarin yake. Muna fata ta duba ta ga cewar ta kawo gyara.

 

Wasu na da tunanin ganin kamar takararka ta hadin baki ne da Gwamnatin APC ta Kano don kar a ce an bar Gwamnan da ke kai ya yi takara shi kadai?

Ba na zaton cewa mutane za su kalleni a haka, saboda na bar tarihi. Daga lokacin da na fara siyasa zuwa yanzu, ni ba a iya hada kai da ni don a yi al’mundahana ko a yaudari al’umma ba, kuma babu wanda zai iya hada kai da ni don neman wannan.

A siyasa banda farashi na neman a ce a ba shi kaza, ko a yi masa kaza don ya yi wani abu. Idan har zan yi haka, wannan cin amanar al’umma ne, kuma ina fata Allah ya tsareni daga aikata hakan.

Hasali ma ba wanda ya taba ji na ina cewa ni wani abu ne na Gwamna, ba wanda ya taba gayyatata mu yi wani abu ma. Abin da muka yarda da shi, bayan Duniya akwai lahira, duk abin da mutum ya yi zai gaya wa Allah.

Ai da a ce Buhari wannan al’mundahanar ya yi, to da yanzu ba a zancensa, dole za a samu mutanen kirki. Muna fata Allah ya sa mu cikinsu.

 

Me ye kiranka ga al’ummar jihar Kano kan wannan takara da kake yi?

Ina kira su sani cewa za mu koma ga Allah, kuma za mu yi wa Allah bayani. Duk wanda za ka zaba, ya zama ka san shi, ka san dalilin da za ka zabe shi.

Mun yarda kowane addini akwai akwai abin da yake da shi, kowane addini  ya zo da wani al’amari da yake jagorantar al’umma ya kai su ga kan daidai. Addini  yana sa k a taimaki Gwamnatinka  ka taimaki rayuwar al’umma, kowane addini yana da kyawawan dabi’u da adalci a shugabanci.

Don haka ina kiran mutane, halin da muke ciki muna da bukatar gyara daga rayuwar dabal-dabal da muke ciki. Ya kamata mu zo mu hadu mu gyara, duk wannan shiru da aka yi, maimakon mu je mu kada jam’iyyar, to gara mu hadu mu ginata mu zabi abin da muke ganin zai amfanemu.

‘Yan APC  da sauran mutane su zo mu hadu don a gudu tare a tsira tare, domin a kafa Gwamnati a Kano ta mara wa takarata baya.

Mun fito takara muna son mu zo mu hadu da su al’umma don mu kwaci kanmu daga halin da ake ciki na gazawa a
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: