Sabon dan was an kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr ta kasar Saudiyya, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa y agama yin duk wani abu da ya kamata yayi a kwallon kafa a nahiyar turai yanzu kuma ya koma Saudiyya domin sake sabuwar rayuwa.
Bayan kasancewar sa wanda ya fi kowanne mutum a duniya yawan magoya baya a Instagram, ya ke kuma da kimanin mabiya miliyan 158 a Facebook, tasirin Cristiano ya kara bayyana bayan komawar sa kungiyar Al-Nassr da ke Saudiyya.
Rahotanni sun nuna cewa Ronaldo yana da magoya baya masu yawan gaske da suke binsa babu dare babu rana sama da kungiyoyin da ya buga wasa a cikinsu a tarihinsa na kwallon kafa.
Ronaldo mai shekara 37 a duniya wanda ya samu rashin jituwa da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, a karshe ya samu wata sabuwar kungiya a gabas ta tsakiya kuma ita ce Al-Nassr.
Gabanin neman da aka yi masa, kungiyar Al-Nassr na da magoya baya kimanin dubu 860, amma da sanarwar komawar sa kungiyar sai magoya bayanta suka karu cikin sa’o’i kalilan.
Kawo yanzu kungiyar na da magoya baya miliyan bakwai da dubu dari shida, sun karu da kusan kashi 90 cikin 100 kuma wannan ba karamar nasara bace da kungiyar ta samu.
Ba dai wannan ne karon farko da kididdiga ta nuna yadda magoya baya ke bin Cristiano ba a kafafen sada zumunta domin lokacin da Ronaldo ya koma Jubentus a kan fam miliyan 100, kungiyar ta samu karuwar mabiya a duka kafafen sada zumunta, sa’annan Real Madrid da ya baro ta yi asarar mabiya sama da miliyan daya cikin awa 24 kamar yadda rahoton jaridar Tifo ya bayyana.
Hakan ya yi matukar tasiri inda Jubentus ta samu karuwa da kusan kashi 25 na magoya baya a duka shafukan ta na sada zumunta kungiyar ta samu sabbin mabiya miliyan shida, wanda wannan ba karamar nasara bace a gareta.
A lokacin magoya bayan sun karu zuwa miliyan 35 a Facebook, a Twitter sun kai miliyan 6.2, yayin da a Instagram suka kai miliyan 15.3 sai dai duk da cewa ana ganin kamar dan wasan na samun koma baya a kwallon kafa a zahiri, amma a shafukan sada zumunta har yanzu shi ne ke da wannan sarautar.
Irin wannan biyayyar da mabiya ke yi, suka nuna wa dan wasan lokacin da yake shirin komawa Manchester United sannan rikicin sa da kungiyar ya haifar da koma bayan mabiya gareta a kafafen sada zumunta.
Da komawar da ya yi Al-Nassr dan wasan zai rika daukar albashin dala miliyan 200 a duk shekara kuma ya zama wanda za’a fi biyan kudi a duk shekara a fagen kwallon kafa a duniya.
wadanda suka fi daukar kudi a duniya kawo yanzu akwai shi Cristiano Ronaldo wanda zai dinga daukar dalar Amurka miliyan 214 sai dan wasan PSG Kylian Mbappe mai daukar dalar Amurka miliyan 63 sai Lionel Messi mai dalar Amurka miliyan 41 sai Neymar shima yana daukar dalar Amurka miliyan 37 sannan kuma sai Andrés Iniesta mai daukar dala miliyan 31