Da farko za mu so ka fada wa masu karatu sunanka
To ni sunana Musa Yusuf an haife ni a garin Gashuwa
Malam Musa mecece sana’arka?
Sana’ata sana’ar aski ce
Anskin gargajiya ko na zamani?
Askin Zamani wanda ake yi da Kilifa
Wa ya koya maka wannan sana’a?
Eh to, wanda ya ko ya min wannan sana’a daga farko sunansa Umar, wani mai gidanmu, wanda kuma shi ne babban yayaynmu a ciki, akwai wani da ake ce masa Abubakar a nan Utako Billage, bayan an gama koya masa shi ne nima aka koya min, lokacin ina makaranta gaskiya na je yadi karatun allo a lokacin, to dawowa ta shi ne aka dauke ni ake koya min bayan shi abubakar an gama yaye shi sai na maye gurbinsa, wato Umar shi ne asalin wanda ya koya min wannan sana’a Allah ya saka masa da alheri.
Ka kai misalin shekara nawa kana wannan sana’ar?
Wannan sana’a zan kai misalin shekara tara zuwa 10 ina yi, saboda na fara yi tun daga 2012 zuwa 2012, na yi karatun Firamare da Sikandire, kuma daga nan ban samu ci gaba ba daga nan na fara wannan sana’a ta aski, lamarin karatu kuma ina nan ina shirye-shiryen komawa.
Kana da aure ?
Eh yanzu ina da aure
Ka kai kamar shekara a Abuja da wannan sana’a?
Na zo Abuja tun 2012 ka ga yanzu kusan shekara bakwai kenan
Ashe ba’a nan ka fara koyon sana’ar ba ko?
A’a ba a nan na koyi sana’ar ba, na zo ne da iyawa ta
A wannan sana’a taku ta aski wane irin ci gaba kake samu?
Gaskiya ina samun ci gaba a wannan sana’a sosai, saboda sana’a ce mai sirri, domin a wannan sana’a na yi abubuwa da daman a ci gaba, na sayi gida na yi aure duk da wannan sana’a, sannan har yanzu ina ci ina sha har ma a kyautta wa wasu da sauransu. Kuma sana’ar nan da ita ce dukkanin wani uzuri da ya taso in har bai fi karfi na ba, to in sha Allahu da ita nake yi, kamar su biyan bukatu da sauransu.
Wadanne irin matsaloli kake fuskanta a wannan sana’a?
Gaskiya ne ko wace sana’a ana samun kalubale a cikinta, amma daga cikin kalubaen da ake samu akwai fannin mu’amala da jama’a, duk abin da aka ce hark ace ta mu’amala da jama’ a to dole sai an samu ‘yan matsaloli, saboda haka sai ka yi hakuri da jama’a, domin za ka batawa wani wani ma zai bata maka, don wanin ma kai baka san ka bata masa ba, don haka dole ka ba wa mutum hakuri. Sannan wani lokacin inji ne zai samu matsala sakamakon rashin wuta da muke fama da shi, sai ka ga mutum ya yi fushi, kuma fa ya san ana rashin wutar nan tun da ba daga Kasar Amurka ko Ingila ya zo ba dan Nijeriya ne, to ka ga a nan ma dole ne sai ka ba da hakuri, wannan shi ne kadan daga cikin kalubalen da muke samu.
A karkashinka a yanzu ka koyar da yara kamar nawa?
Eh to yaran da suka koyi aiki a wurina guda biyu ne, su kawai na taba koyarwa gaskiya.
To na ga kamar mutum uku a shagonka, daga cikinsu akwai wadanda ka koyar da su aikin?
A’a wadannan duk da iyawarsu suka zo ba ni na koya masu aiki ba, don Oga gaba daya shi yakawo su, na zama dai kawai nine nake jagorantar shagon ne gaba daya.
To wane kira za ka yi ga mutanen da suke zuwa Abuja su zauna zaman kashe wand aba sana’a?
Eh, gaskiya wannan kalubale ne mai karfi a gabansu, don wannan babbar matsala ce a ce mutum ya zo Abuja kawai ba shi da aiki sai ya ci ya kwanta gari yaw aye ya shiga yawonsa, wannan duk ba za ta fitar da mutum ba. Dukkanin wanda ya san ya baro garinsu ya zo Abuja, to kamata ya yi ya tsaya tsayin daka ya tsaya da kafarsa, saboda Abuja ba wurin takala ba ne kawai don ya kama bushasha da sauransu, gari ne wanda idam mutum ya zo to ya rika sanin ina dare ya yi masa.
Rashin hakan ne yake sawa ka gamutum ya samu matsala daga nan sai ya fada shaye-shaye, kuma a lokacin da zai bar kauyensu ba ya shan komai, amma sakamakon zuwansa nan sai ka gay a biyewa ‘yan Kasa a shiga nan a fita can, dai ga matasa ba hanya ce mai bullewa ba. Ya kamata a ce mutum ya yi hankali da kansa, sannan kuma kula da kyau.
To a karshe wane kira za ka yi wa abokan irin wannan sana’a taka?
Kiran da zan yi wa abokan sana’ata shi ne, ina ba su shawarar su jure, don wannan sana’a juriya take bukata, don gaskiya tana bukatar juriya ta tsayiwa, da juriya ta kula da wuri, da juriya ta kula abokin hulda wato ‘Customer’ kenan da sauransu. Kuma sannan ana bukatar tsaftar a wannan sana’a sosai, yana da kyau mutum ya zama maia tsafta koda yaushe.
Sannan kara ba da shawara ga abokan wannan sana’a tawa, da cewa dukkan abin da zai kawo matsala tsakaninsu da yaran shagonsu to su nisace shi. Babbar matasalar da ake samu tsakanin yaro da mai gida ana yawa samun sabani, sakamakon su yaran basa nuna biyayya ga masu gidan nasu, domin yaro ne da ka fara koya masa aski ya gay a dan fara iyawa hannunsa ya fara tsayawa, kawai sai ya rika nuna maka cewa shi ma ya tsaya da kafarsa. To don haka a dinga yin hakuri da juna.
A irin shirin koyar da sana’o’i da Gwamnati ke yi wa matasa, an taba turo muku dalibai don ku koya masu wannan sana’a?
A’a gaskiya wannan sakon har yanzu ba karaso gareni ba, mu dai jin labarin yadda ake rarraba yara a koya masu, sai dai mu har yanzu abin bai zo nan ba.
Kamar wani uba ko dai wata haka ba wanda ya taba kawo dansa don koyon wannan sana’a?
Eh akwai wasu yara da aka kawo, ko da yake ba ni na koya masu gaba daya ba, amma dai akwai tawa gudunmawar a ciki. Wanda ya koya min aikin shi ya koya masu, kuma duk kusan aikin ma nina yi amma dai a hannuna a danka sub a, kuma har yanzu suna nan suna yi, kuma ‘ya’yan yayammu ne gaba dayansu, kuma muna tare da su a nan.
To wa zaka gode wa kafin mu rufe hirar?
AIlah da manzonsa da iyayena da kuma Umar da ya koyamin wannan sana’a duk Allah ya saka musu da alheri.