Dakarun Sojin Saman Nijeriya (NAF) sun kashe aƙalla ’yan ta’adda 35 a harin sama da suka kai iyakar Nijeriya da Kamaru.
Mai magana da yawun NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce sun kai harin ne da sassafe a ranar Asabar, 23 ga watan Agusta, 2025, ƙarƙashin Operation Hadin Kai (OPHK).
- Amfani Da Rashin Amfanin Auren Jari
- CMG Ya Yi Bikin Cudanyar Al’adu Mai Taken “Sautin Zaman Lafiya” A Hadaddiyar Daular Larabawa Da Koriya Ta Kudu
Ya bayyana cewa ’yan ta’addan sun taru a kusa da iyakar bayan sun yi ƙoƙarin kai wa sojojin ƙasa hari a yankin Kumshe.
Bayan samun bayanan sirri, NAF ta kai hare-hare a wurare huɗu da aka gano, inda ta kashe sama da ‘yan ta’adda 35.
Bayan kammala aikin, sojojin ƙasa sun tabbatar da cewa an kwantar da tarzomar a yankin.
Ejodame ya ƙara da cewa rundunar sojin sama za ta ci gaba da tallafa wa sojojin ƙasa tare da tarwatsa ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.
Shugaban sojin sama na ƙasa, Air Marshal Hasan Bala Abubakar, ya yaba da ƙwarewar dakarun tare da tabbatar da cewa za su ci gaba da kai hare-hare bisa bayanan sirri domin murkushe ’yan ta’addan da ke barazana ga tsaron Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp