Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC), ta rufe wani babban kanti na ‘yan China da ke unguwar Wuse 2 a Abuja, bisa zargin sayar da kaya masu tambari da harshen China ba tare da izinin hukumar ba.
Daraktan bincike na NAFDAC, Shaba Mohammed ne, ya bayyana wa manema labarai cewa galibin kayan da ake sayarwa a kantin sun ƙunshi tambari da rubutu cikin harshen China, wanda ya saɓa wa dokokin ƙasa.
- Cece-kuce Kan Badaƙalar Kuɗaɗe A NNPCL: SERAP Ta Bukaci Mele Kyari Ya Yi Bayani
- Gwamnan Bauchi Ya Sauke Kwamishinoni 5, Ya Naɗa Sabbi 8
“Za mu binciki sama da kashi 90 na kayan da ke cikin wannan kantin don gano yadda aka shigo da su cikin ƙasar nan,” in ji Shaba Mohammed.
Ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin kayan da ake sayarwa a kantin sun ƙare wa’adin amfaninsu, amma har yanzu ana ci gaba da sayar wa jama’a.