Daga Fatima Muhammad Ali, Abuja
A jiya Laraba ne, aka kammala shirye-shirye tsakanin kamfanin buga jaridun LEADERSHIP da fitacciyar ’yar wasan Hausa, wacce kuma ta yi suna wajen fita a matsayin mai hakuri a finafinanta, wato Nafisa Abdullahi, inda ta zama Jakadiyar LEADERSHIP A YAU.
Bayan kulla wannan yarjejeniya, Nafisa Abdullahi ta bayana cewa, “da farko dai ina mika godiya ta ga Kamfanin Rukunan Jaridun LEADERSHIP. Na yi mutukar farin cikin kasancewa ni ce Jakadiyar LEADERSHIP A Yau ta farko. Yadda aka dauke ni da muhimmanci ne ya sa har ake so a mayar da ni Jakadiya Jaridar LEADERSHIP A Yau. Duk a tarin Jaruman da suke Nijeriya, an dauke ni, ni ce ta farko wanda aka ba ta wannan babban matsayi. Don haka ina mutukar farin ciki.”
Ta ci gaba da bayyana cewa, “lalle zan bada karfin gwiwa don in ga wannan alakar tamu ta dore fiye da yadda muke tunanin za mu samu .”
Da yake nuna jin dadinsa da wannan hulda, Mukaddashin Manajan Daraktan sashen LEADSRSHIP A YAU, Stanley Kingsley Nkwocha ya nuna matukar jin dadinsa da wannan dangantaka da Jarumar, inda ya yi fatan cewa wannan huldar jakadanci za ta zamam hanyar da za a amfani juna tsakanin Jarumar da kuma LEADERSHIP A YAU.