Abin mamaki baya karewa a wannan duniyar. Wata yarinya ‘yar shekara 13 da ta mutu sakamakon cutar kumburin jijiyar kwakwalwa, ta taimaka wurin bayar da gudummawar sassan jikinta ga mutum takwas, adadi mafi yawa a tarihi.
Jemima Layzell, wacce ‘yar asalin yankin Somerset ce da ke London, ta rasu a 2012, ta bayar da gudummawar zuciya, tumburkuma, huhu, kodoji, karamin hanji da hanta ga yara biyar.
Iyayen Jemima sun ce marigayiyar na da basira da tausayi kuma Allah ya ba ta fikira – a dalilin haka ne ma suke matukar alfahari da wannan abin tarihi da ta aikata.
Hukumomin lafiya sun ce babu wani mutum da ya taba bayar da gudummawa ga mutane da yawa kamar Jemima.
An yiwa mutum uku dashen zuciya da ‘yan hanji da tumburkumarta a lokaci guda kuma mutum biyu suka samu kodojinta.
An raba hantarta inda aka dasawa mutum biyu, sannan kuma wani mara lafiya ya samu gudummawar huhunan da ta bari.
Akasari dai, ba a cika samun irin wannan gudummawa ga adadin mutane masu yawa haka ba.
‘Ta musamman ce kuma ba irinta’
Mahaifiyar Jemima, Sophy Layzell, mai shekara 43, kuma mai koyar da wasannin kwaikwayo da mahaifinta Harbey Layzell, dan shekara 49, kuma manajan darakta a wani kamfanin gine-gine, sun ce sun san Jemima na son ta bayar da gudummawar sassan jikinta. Saboda sun yi magana akan haka kwanaki kalilan kafin mutuwarta, bayan wani mutum da suka sani yayi hatsari ya mutu.
Sophy ta ce Jemima ba ta taba jin batun bayar da gudummawar sashen jiki ba kafin wannan lokaci, kuma ta yi ta dar-dar, amma dai ta fahimci muhimmanci abin.”
Ta ce har yanzu suna jin bayar da gudummawar sassan jikin ‘yarsu, shawara ce mai wahala amma dai ita ce daidai.
A cewarta idan muka ce a’a, tamkar mun hana wa sauran mutum takwas damar rayuwa. Duk iyaye suna iya cewa a’a, don kuwa Allah ya yi mu ne mu kare ‘ya’yanmu. Kawai dai mun kwan da sanin cewa Jemima ta amince a yi hakan shi ya sa muka ce eh.
Cibiyar kula da ayyukan dashe da karin jiki ta shirin inshorar lafiya a Ingila ta ce daruruwan mutane ne har yanzu ke mutuwa ba gaira ba dalili a lokacin da suke jiran a yi musu dashe, don kuwa iyaye da dama suna kin bayar da gudummawa.
Rahoton kafar BBC ya nakalto cewa; A bara, mutum 457 ne suka mutu lokacin da suke jiran samun dashe a cikinsu 14 kananan yara ne. A yanzu haka akwai mutum 6,414 da ke cikin jerin wadanda ke jiran samun gudummawa kuma sun hada da yara 176.
A shekara ta 2015, wani matashi da ya mutu Tom Wilson mai shekara 22 sakamakon tsurewar da ya yi bayan sandar kwallon hockey ta same shi a ka. An kiyasta cewa gudummawar sassan jikinsa da ya bayar, ciki har da fata da kashi da bargo ta taimaka wa rayuwar kimanin mutum 50.