Hausawa su kan ce, da abokin daka a kan sha gari. A ganina, wannan karin magana ya bayyana yanayin huldar dake tsakanin Sin da Najeriya. Matukar an lura da hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen 2, to, za a rika ganin labarai masu kyau a kai a kai.
Za mu iya daukar wasu abubuwan da suka faru a kwanan nan a matsayin misali. Da farko dai, a karshen bara, babban bankin kasar Sin da babban bankin Nijeriya, sun sabunta yarjejeniyarsu ta musayar kudaden kasashensu da jimillarsu ta kai RMB yuan biliyan 15, ko kuma kudin Nijeriya kimanin Naira tiriliyan 3 da biliyan 280, inda aka samu wani sabon wa’adin yarjejeniyar na shekaru 3. Hakan zai fadada amfani da kudin kasa a cikin gida tsakanin Sin da Nijeriya, da saukaka harkokin cinikayya, da zuba jari, da hadin kai a fannin hada-hadar kudi tsakanin sassan biyu, da tinkarar kalubalen hawa da saukar darajar musayar kudi a kasuwannin kasa da kasa.
- Da Ɗumi-ɗumi: Majalisar Dokokin Legas Ta Tsige Kakakinta
- Gwamnan Zamfara Ya Jajanta Wa Iyalan Da Harin Jirgin Sojoji Ya Rutsa Da Su
Na biyu shi ne, a kwanan baya, bankin CDB na kasar Sin ya samar da rance a zangon farko, wanda yawansa ya kai Euro miliyan 245, domin ci gaba da aikin gina layin dogo tsakanin jihohin Kaduna da Kano na arewacin Najeriya. Wani kamfanin kasar Sin ne ke daukar nauyin shimfida layin dogon da tsawonsa ya kai kilomita 203, wanda zai saukaka tafiye-tafiyen al’ummar arewacin Najeriya, bayan da aka kammala aikin ginin layin dogon.
Na uku shi ne, karuwar cinikayyar da ake yi tsakanin Sin da Najeriya, ta sa wani kamfanin jigilar kayayyaki ta jiragen ruwa na kasa da kasa ya kaddamar da wani layin jigilar kaya kai tsaye tsakanin birnin Shanghai na Sin da Lagos na Najeriya, a farkon watan da muke ciki. Layin zai takaita lokacin jigilar kaya tsakanin biranen 2 zuwa kwanaki 27, kana farashin hidimar jigilar kayan ma ya ragu.
A sa’i daya kuma, manyan jami’an kasashen 2 suna cudanya da juna sosai. Misali, a kwanan baya, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya kammala ziyararsa a Najeriya. Sa’an nan a jiya, darekata janar mai kula da huldar abota tsakanin Najeriya da Sin, wadda ta shafi manyan tsare-tsare a dukkan fannoni na tarayyar Najeriya, Joseph Tegbe, shi ma ya isa birnin Beijing na Sin, inda ya fara wata ziyara a kasar.
Watakila za ka so ka san dalilin da ya sa ake samun cudanya sosai tsakanin Sin da Najeriya, kana huldar dake tsakaninsu na da kyau matuka?
Dalili na farko shi ne, kamar yadda ministan wajen kasar Najeriya, Yusuf Tuggar ya fada, yayin da yake ganawa da Mista Wang Yi a wannan karo, wato “Ba wani bambancin ra’ayi tsakanin Najeriya da Sin.” Hakika, kasashen Najeriya da Sin, bisa matsayinsu na manyan kasashe da tattalin arzikinsu ke kan hanyar ci gaba, suna da buri iri daya, wato zamanantar da kansu, da kyautata zaman rayuwar jama’a. Kana sam ba sa sha’awar ra’ayin kasashen yamma na ja-in-ja a fannin siyasa a duniya.
Ban da haka, Najeriya da Sin suna da moriya ta bai daya. Inda kasar Sin ke kokarin hada manufofin raya kasa da ta gabatar, da shirin raya tattalin arziki na Najeriya, don biyan bukatun Najeriya na samun ci gaba, da tabbatar da moriyar kamfanonin Sin a lokaci guda.
A nan gaba, yayin da ake kokarin gina yankin ciniki mai ‘yanci na nahiyar Afirka, Najeriya a bisa matsayinta na babbar kasa, da tattalin arziki mai karfi, tabbas za ta iya amfani da fifikonta a fannonin kayayyakin more rayuwa, da albarkatun kasa, da fasahohi, gami da jari, wajen jagorantar aikin cin gajiyar kasuwannin yankin da take ciki. Yayin da hadin gwiwar Sin da Najeriya zai iya taimakon Najeriya wajen taka muhimmiyar rawa a fannin raya yankin da take ciki, tare da haifar wa kamfanonin Sin masu zuba jari da riba. Tabbas wannan makoma mai haske, ita ce babban dalilin da ya sa ake samun dangantaka mai kyau tsakanin Najeriya da Sin. (Bello Wang)