Fadar shugaban kasa ta ce babu wanda zai iya ikirarin cewa shi ne ke da alhakin nasarar zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015.
Fadar tayi wannan martanin ne yayin da jigo a jam’iyyar APC kuma Dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar a 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce in ba don shi ba, da Shugaba Buhari bai ci zaben shugaban kasa a 2015 ba.
Tinubu yayi magana ne a ranar Alhamis din da ta gabata a wani taro da wakilan jam’iyyar APC a jihar Ogun.
Tinubu ya yi magana kan yadda ya mika Yemi Osinbajo a matsayin mataimakin shugaban kasa, a lokacin da aka nuna adawa da kin amincewa ayi takarar Muslim-Muslim (Shugaban kasa musulmi Kuma mataimaki musulmi) a jam’iyyar APC.
Sai dai mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce watakila ba abin mamaki ba ne a jajibirin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC akwai wadanda suka yi tsayin daka wajen ganin an lashe zaben, shekaru bakwai da suka wuce.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp