ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nasarar Tsarin CBN Na Samar Da Kudaden Habaka Tattalin Arzikin Nijeriya

by Leadership Hausa
3 years ago
CBN

A daukacin fadin duniya manyan Bankuna na bayar da gagarumar gudunmawa wajen habbaka wa da kuma bunkasa tattalin arzikin kasashe ta fannoni da dama.

A zahiri suna bayar gudunmawar ce saboda irin wadannan Bankunan nan ne makura wajen bayar da rancen kudade, kirkiro da tsare-tsaren kudade, musamman ganin cewa, irin wannan bankunan na a karkashin Gwamnati su ne ke tabbatar da samar da daitaito a tsare-tsaren hanyoyin da suka dace a tunkara don samar da canje-canjen sa suka kamata ga fannin tattalin arziki.

  • Asalin Abin Da Ya Sa Jama’a Ba Su Ganin Alfanun Tallafin Mai – Dakta Yakubu
  • ‘Yan Boko Haram Sun Kashe Masunta A Tafkin Chadi

Alal misali, a Nijeriya, dora Godwin Emefiele a matsayin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN za a iya cewa ya zuwa yanzu, kwaliiya ta biya kudin sabulu domin da hawarsa karagar shugabancin CBN ya kara inganta ayyukan Bankin, musamman ta hanyar inganta tsare-tsaren samar da kudade, inganta kasuwanin hada-hadar kudade da samar da hanya mai sauki don karbar kudade daga CBN don zuba jari a fannin kasuwanci ta hanyar samun rancen kudade daga CBN.

ADVERTISEMENT

Daukin da Emefiele ya samar a bangaren harkokin Bankuna ya taimaka wa Gwamnatin matuka, ya na da kyau a sanar da cewa, koda yake irin wannan daukin na samar da kudade ba sabon abu ba ne domin an faro hakan ne tun a shekarar 1920.

Bugu da kari, akasarinManyan Bankuna da ke a kasashen da suka ci gaba suna samar da saukakar hanyoyi don bayar da goyon baya ga farfado da tattalin arzikinsu, inda alal misali, ko a shekarar 2008 zuwa 2009, irin wadannan kasashen sun taka muhimmiyar rasa wajen tsamo kasashen su daga matsayin tattalin arziki da da suka tsinci kansu a ciki da kuma a lokacin da duniya ta fuskanci kalubalen bullar annobar Korona, wanda samar da kudade na daga cikin dabarun da kasashen ke yi suna yi ne, don kara bunkasa tattalin arzikinsu.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Baro Brazil Bayan Halartar Taron BRICS Na 2025

Kuratan Sojoji 1,196 Aka Yaye A Makarantar Horar Da Sojoji Ta Zariya

A bangaren Gwamnati mai ci a yanzu, ta samar da dauki na zuba sama da Naira Tiriliyan 3, inda wadannan kudaden suka taimaka wajen kara samar da ayyukan yi da kuma da kara bunkasa tattalin arzikin kasar nan, inda hakan ya sa CBN tun a shekarar 2015, ya na ci gaba da kirkiro da shirye-shirye iriiri na samar da dauki yadda tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da tafiya yadda ake bukata.

Misalin, CBN ya kirkiro da tsarin (PPP) wanda za a mayar da hankali wajen karfafa kamfanonin cikin gida don ci gaba da sarrafa kaya a cikin kasar nan, wanda kuma hakan zai rage yawan shigo da kaya daga ketare da kara samar da aikin yi ga ‘yan Nijeriya da sauransu Har ila yau, a ranar 31 zuwa 28 na watan Janairun ne a babban bankin kasa CBN da ke Abuja aka kaddamar da mika Cakin Banki na jimllar Naira biliyan 23.2 ga bankunan kasuwanci bakwai da suka shiga cikin shirye-shiyen sa, inda su kuma wadannan Bankunan da suka amfana, za su yi amfani da wasu daga cikin kudaden wajen habbaka ayyukan su, samar da ayyukan yi a ‘yan kasar da sauransu.

Hakazalika, bisa wata kididdiga da aka samo daga CBN ta nuna cewa, CBN ya samar da daukin kudade ga fannin kerere da suka kai na jimllar Naira biliyan 803.36 inda tuni an zuba wadannan kudaden a cikin ayyuka 228 daban-daban da suka hada da Noma, Hakar Ma’adanai, inganta masana’antu da sauransu.

Haka kuma, CBN a watan Mayun 2020 ya gabatar da tsaretsaren wanzar da samar da dauki bayan bullar annobar Korona a kasar nan, wanda daya daga cikin manufar haka ita ce don a cike gibin da ake ganin bullar annobar za ta haifar ga fannoni daban-daban na tattalin arzikin Nijeriya da kuma masana’antu masu zaman kansu dake a kasar.

Kafin Godwin Emiefele ya samar da wannan daukin, fannin kere -kere na Nijeriya na samar da kasa da kashi 15 ne kacal ne a cikin dari, ga tattalin arzikin Nijeriya, inda hakan ya nuna babbar damuwar, ita ce yadda aka ci gaba da shigo da kaya daga ketare bayan alhali Nijeriya na da karfin da za ta iya sarrafa kaya har ta fitar zuwa ketare.

Har ila yau, tsarin da Emefiele ya kirkiro ya kara inganta dangantaka da Bankunan hada-hadar kudade na DMB da kuma a tsakanin sauran Cibiyoyin hada-hadar kudade inda daukacin su suka mayar da hankali a fannonin aikin noma, fannin kere-kere.

Bugu da kari, a karkashin samar da ainihin kayan aiki wato a Turance, (RSF), CBN ya zuba jimllar Naira tiriliyan 1.40 zuwa Naira tiriliyan 331, musamman domin amfani da kudaden a fannin aikin noma da fannin

ma’adanai da sauransu, inda kuma a daukin da CBN ya samar a shirin (RSSF), ya zuba Naira biliyan 166.21 don yin ayyyuka guda 25.

CBN ba wai ya mayar da hankali ne wajen samar da daukin kudade ba ne kawai, har da kuma wayar da kan masu bukatar zuba jari domin su zuba nasu jarin a fanoni don a kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.

Har ila yau, a daukin da CBN a watan Afirilun 2022, ya samar biyo bayan bullar annobar Korona a kasar nan, ya dauki matakai da dama na fadada samar da dauki a fannin kiwon lafiya, inda CBN ya fitar da Naira biliyan 93 don a kara habaka fannin da kuma gudanar da ayyukan da ake sa burin cimma a kasar.

Manufar shirin shi ne, samar da bashi ga kamfanonin cikin gida da ke sarrafa magunguna, inda kuma tsarin ke bukatar ganin an kara samar da masu zaman kansu da ke son zuba jari a fannin kiwon lafiya, musamman don a rage yawan ‘yan Nijeriya da ke fita zuwa ketare neman lafiya.

Babban misali a nasarar da CBN ya samar a fannin na inganta kiwon lafiya a kasar shi ne, yadda a kwanan baya Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo yaje wani Asibitin da ke a cikin kasar nan don a duba lafiyarsa.

Wannan ya nuna a zahiri tsarin na Emefiele ya nuna akwai bukatar a kara wa bankunan kasuwanci na kasar kwarin gwiwa don su hadaka da masu son zuba jari a daukacin fannonin tattalin arzikin Nijeriya, kamar yadda Emefiele ke yawan yin kiraye-kiraye akai.

Akpan mazauni ne a garin Kalaba mai kuma yin fashin baki a kan tattalin arziki.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu Ya Baro Brazil Bayan Halartar Taron BRICS Na 2025
Labaran Kasuwanci

Tinubu Ya Baro Brazil Bayan Halartar Taron BRICS Na 2025

July 12, 2025
Kuratan Sojoji 1,196 Aka Yaye A Makarantar Horar Da Sojoji Ta Zariya
Labaran Kasuwanci

Kuratan Sojoji 1,196 Aka Yaye A Makarantar Horar Da Sojoji Ta Zariya

June 21, 2025
Za Mu Tabbatar Da Samun Kyakkyawar Alaka Da Gwamnati Don Ci Gaban Kasuwar Kofar Ruwa – ‘Yanleman
Labaran Kasuwanci

Za Mu Tabbatar Da Samun Kyakkyawar Alaka Da Gwamnati Don Ci Gaban Kasuwar Kofar Ruwa – ‘Yanleman

January 11, 2025
Next Post
Me Ya Sa Ba A Fara Shekarar Hijirah Da Ranar Badar Ko Ranar Cikar Wahayi Ba? (I)

Me Ya Sa Ba A Fara Shekarar Hijirah Da Ranar Badar Ko Ranar Cikar Wahayi Ba? (I)

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.