Connect with us

NAZARI

Nasihar Uwa Ga ‘Ya Lokacin Da Za Ta Yi Aure

Published

on

‘Ya ke ‘yata amarya, ga wasu hudubobi guda goma da ni ke son ki dauke su don su

zama tsarabar ki ta zuwa gidan miji, tafiya da su ba karamar gara bace a gare ki.

 

Su Ne Kamar Haka:

1) Biyayya Ga Miji: Ki sani wajibi ne gare ki, ki yi biyayya ga mijin ki matukar ba a kan sabon Allah ba ne. Hikimar haka kuwa ita ce, mijinki zai kara jin kaunarki a ransa, kuma ‘ya’yan da za ku haifa za su taso cikin biyayyar iyayensu da kuma junansu, kai har ma ga Al’ummar.

 

2) Kishin Kanki Ga Mijinki: Ma’ana ki zama mai kamewa da barin duk wani namijin da ba mijinki ba. Ba sakin fuska balle raunana murya ko sakin jiki ga wani kannen miji, ko abokin miji don yin hira barkatai. Hikimar kiyaye hakan kuwa ita ce; mijinki zai kara samun natsuwa da yarda da ke, kuma za ki kare kanki daga dukkan wata kafa da za ta haddasa ma mijinki rashin yarda da ke.

 

3) Kada Ki Fita Sai da Izininsa: Wajibi ne ki zama mai tabbata a gidan mijinki, ba mai leke ko yawan shiga makwabta ba. Fita ma sai da izininsa komin muhimmancin fitar a gare ki. Ki sani fita bada izinin miji ba tana da zunubi mai girma a gurin Ubangijinmu Allah. Hikimar hakan kuwa shi ne, zai san ina za ki je, yaushe za ki dawo, zai iya ma kaiki ko ma ya sa wani ya raka ki. Ba dabara ba ce ki rika fita ko yaushe kika ga dama kamarb wata Akuyar sake, domin yin hakan shi ma rashin kamunkai ne.

 

4) Kada Ki Juya Masa Baya Yayin Ibadar Aure: Ki sani wajibi ne a gare ki, ki biya ma mijinki bukatarsa ta shimfida a duk lokacin da ya neme ki, matukar ba a lokutan da shari’a ta hana a sadu ba, irin lokacin al’ada, da lokacin jinin haihuwa, ko kuma lokacin Azumin Ramadan da rana. Hikimar da ke cikin kiyaye bukatar mijinki kuwa ita ce, za ki kawar masa da sha’awarsa ta hanyar halal, kuma kin kare shi daga fadawa hanyar zina da matan banza a waje, kuma ke ma kin samu lada. Har wayau idan rabo ya shiga a lokacin ke ma kin bada gudunmawa ga yaduwar Al’ummar Annabi Muhammadu (SAW) ta hanyar sunnarsa, ba ta hanyar shedan ba.

 

5) Ki Zama Mai Wadatuwa: Yana da kyau ki wadatu da abin da mijinki ya kawo maki komin kankantarsa, kuma ki zama mai la’akari da matsayinsa. Watau dai kada ki kallafa masa abin da ba zai iya ba. Ki sani Allah ma bai yi mutane duka daya ba. Don haka bukata ma ba za ta zama daya ba. Hikimar yin haka kuwa ita ce za ki samu karin daraja a gun mijinki, kuma za ki sa ya zamana komi ya samu ba inda zai yi tunanin kaiwa sai gida, don ya san zaki karba hannu bibbiyu a mutunce.

 

6) Yin Tattali: Ya dace matukar dacewa ki rika tattala abin da mijinki ya kawo maki don amfani. Ki rika tattali don yinsa hanyar karfafawa mai gida gwiwa ce ya kara kaimin nema, domin yana da yakinin ba aikin banza ya ke yi ba, ya san za ki tattala shi ya yi amfani mai yawa kuma ba almabazzaranci ko barna. Hikimar haka kuwa ita ce, za ki zama kullum abin tunanin mijin ki da zarar ya samo wani abu mai muhimmanci, domin ya san yana kawo sa gida kin san yanda za ki tattala shi ya amfani dukkan iyali.

 

7) Yin Godiya: Lalle ki zama mai yawan godewa mijinki. A duk lokacin da ya yi maki wani alheri, ko ya yi wa ‘ya’yanki ko ‘yan’uwanki, to ki karba hannu bibbiyu, ki yaba kuma ki gode masa. Hikimar haka ita ce, dukkan wanda ake gode masa, an sa masa daukin da kaimin ya kara karowa ne ba gajiyawa. Kuma ko Ubangijinmu Allah yana son a gode masa, idan kuma aka gode masa (Allah) shi ma karowa ya ke yi, ballantana mutane.

Kwantar Da Kai Ki Zama Na Matar Da Ta Iya Kwantar Da Kai Da Rarrashi Ga Mijinki: Kar ki zama mace mai saurin harzuka da tsagalgalewa ko yi masa magana gatse-gatse, ba ladabi ko nuna girmamawa. Hikimar kwantar da kai kuwa ita ce, za ta sa mijinki ya kara sonki ya kaunace ki ko da yaushe, kuma za ta dallashe masa kaifin yawan ganin kuskurenki a ko da yaushe.

 

9) Kiyaye Fushin Miji: Lalle ne ki san abubuwan ko halayyar da ke sa mijin ki yin fushi ko tunzura shi. Misalansu kuwa su ne, rashin gama abinci da wuri, damunsa lokacin da ya ke hutawa daga aiki, yin bacin rai lokacin da ya ke cikin farin ciki, ko yin farin ciki a yayin da ya ke cikin bacin rai, da dai sauran ire-irensu. Hikimar kiyaye fushin miji kuwa ita ce, za ki samu karin kauna ga mijinki idan ya fahimci kina kiyayewa ga abin da zai sa shi fushi, ko kiyaye abin da za su haddasa masa damuwa ko bacin rai, shi ma zai rika kiyaye naki fushin, kuma za ku zauna lafiya.

 

10) Kyautata Wa Makusantansa: Makusantan mijin ki su ne, iyayensa, dangi da ‘yan’uwansa, iyalinsa da barorinsa, abokansa ko abokan huldarsa. Dukkan su wajibi  ne a gare ki ki rika kyautata masu ta hanyar da ta dace, kuma ki yi kokarinki da damar da mijinki ya baki don kyautata masu. Kar ki zama mai rowa ko hadama balle hamdama da babakere akan kaya ko arzikin mijinki, don ganin kina  matarsa.Ki sani suma suna da hakki a kansa, sai dai ke kin fi su dammar aiwatarwa. To ki yi amfani da damarki ki domi kyautata alakarki da zamantakewarki da su, ba reni, ba wulakanci a sakanin ku.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: