Mene ya haddasa rikicin Rasha da Ukraine? Dalilin shi ne yunkurin NATO na neman fadada ikonta zuwa gabashi.
Sanin kowa ne cewa, an kafa NATO ne bisa ra’ayin yakin cacar baka, kuma tun lokacin kafuwarta ta zama jigon tallafawa Amurka wajen yin babakere a duniya. Yau sama da shekaru 30 ke nan da kawo karshen yakin cacar baka, sai dai wannan kungiya tana ci gaba da kallon duniya da ra’ayin yakin cacar baka, har tana yunkurin fadada ikonta zuwa yankin Asiya da Pasifik. Kwanan baya, an kira taron koli na NATO a Lithuania, kuma kafin bude wannan taro, babban sakantaren kungiyar Jens Stoltenberg ya ce, tsaron NATO ba ma kawai ya shafi harkokin shiyya ba, har ma ya shafi duniya baki daya, wannan ya sa taron ya gayyaci shugabannin kasashen Japan da Koriya ta kudu da Austriliya da New Zealand. Amma wasu kasashe ciki har da Faransa sun ki amincewa da shawarar kafa ofishin kungiyar a kasar Japan, saboda a ganinsu Japan tana tekun Pasifik, kuma NATO kungiya ce da ta shafi yankin arewacin tekun Atlantika.
NATO ba ta san matsayinta ba, tana ikirari cewa, ita kungiya ce ta shiyya, kuma kungiya ce mai kare kanta, amma kuma ta keta ka’idojinta, inda take yunkurin fadada ikonta zuwa shiyyar Asiya da tekun Pasifik tare da zuga sauran kasashe mambobi da su kara kasafin kudi da suke warewa a fannin soja. Haka kuma NATO ta yi biris da dokar kasa da kasa da ka’idar huldar kasa da kasa, ta tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe, tare da sa hannu cikin yake-yake da dama. Ban da wannan kuma, tana kokarin kafa kungiyoyin kawance, da haddasa gaba da juna.
Yankin Asiya da Pacific, yanki ne na yin hadin gwiwa da samun ci gaban juna, a maimakon wuri na yin fito na fito. Don haka, ko kadan ba za a amince da yunkurin NATO na fadada ikonta zuwa shiyyar Asiya da tekun Pasifik ba. (Mai zana da rubuta: MINA)