A karo na biyar yau nake gabatar da nazari kan jerin littattafan da Mai shari’a, Khadi Muhammad Uthman El-Mainari na Kotun Daukaka Kara ta Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi yake wallafawa a salon bayar da labari irin na Magana Jari Ce na marigayi Malam Abubakar Imam.
A baya mun yi nazarin littafin Baba Zube na Daya zuwa na Hudu a jaridar Aminiya. To a yau ga nazari kan littafi na biyar mai sunan: Baba Zube (Gwamnati).
- Sojoji Sun Kama ‘Yan Ta’adda 25, Sun Ceto Mutum 16 Da Aka Sace
- Matashi Ya Kashe Kakanninsa Kan Abinci A Kano
Littafin yana da shafuka 145 na tsantsan labarai, amma kafin nan yana da bango da mai bi masa da ya kunshi Hakkin Mallaka da shekarar bugawa da kuma madaba’a da adireshinta. Sai shafi na gaba dauke da sadaukarwa ga tsohon Babban Jojin Nijeriya, Mai shari’a Ibrahim Muhammad Zango, (mai ritaya), wanda marubucin ya ce, ya sa shi a aikin gwamnati, kuma ya yi masa nasiha da ya rike aiki da amana da gaskiya.
Sai shafin da aka ware don sharhi a kan littafin, sannan sai na kunshiyar abubuwan da ke cikin littafin Wadda take da sassa takwas.
Sashe na farko wanda ya fara daga shafi na 1 zuwa na 10, Baba Zube ne yake bayar da labarin wani taron da aka gayyace shi don ya gabatar da jawabi ga ma’aikatan leken asiri na cikin gida don tabbatar da tsaro da zaman lafiyar kasa. Sananne ne cewa babban nauyin da ke kan kowace gwamnati na farko, shi ne samar da tsaron rayuka da lafiya da dukiyar al’umma kafin komai. Ina kyautata zaton wannan ne ya sa mawallafin littafin ya sa masa wannan suna na ‘Gwamnati’ domin in aka rasa tsaro a kasa daidai yake da an rasa gwamnatin.
Da Baba Zube ya mike don yi jawabi bayan an gabatar da shi, sai ya yi waiwaye Wanda masu iya magana suka ce, adon tafiya. Ya kawo takaitaccen bayani kan gwamnati a kasar da yau ake kira Nijeriya. Ya tabo, Daular Usmaniyya mai hedikwata a Sakkwato, wadda kuma ita ce daula ta karshe da Turawa suka rusa a kasar nan. Kuma ya bayan cewa Daular Borno da ta Kwararrafa ne kawai a Arewa ba su cikin Daular Usmaniyya. Sai Kudu maso Yamma da ya zauna a karkashin Daular Yarbawan Oyo. Kudu maso Kudu kuma Daular Benin, yayin da Yankin Kudu maso Gabas ke rayuwa karkashin kananan sarakunan kabilar Ibo. Ya yi takaitaccen bayani kan yadda Turawan Mulkin Mallaka suka ci daulolin da yaki, inda sula cinye yakin Kudu tun kafin 1900, amma Arewa sai a 1904 suka rusa Daular Usmaniyya suka kashe Sarkin Musulmi Attahiru a garin Burmi da ke Jihar Gombe ta yanzu.
Ya yi bayanin yadda Turawan suka ci gaba da mulki rara-gefe, wato ta amfani da sarakuna, musamman a Arewa inda ake da tsarin gudanar da mulki hawa-hawa ga kurkuku ga masana’antu da wayewa da ilimi da sauran abubuwan ci gaba.
Daga nan ya yi bayanin ire-iren tsare-tsaren mulkin da Turawa suka yi tun daga hade Arewa da Kudu a 1914 har zuwa bai wa Nijeriya ‘yanci a 1960.
Sai kuma gwamnatocin da aka yi daga samun ‘yancin kai da kutsawar sojoji a cikin mulkin har zuwa 1999 da aka dawo mulkin farar hula.
Sai Baba Zube ya ce, dukan wadannan gwamnatoci manufarsu daya ce, ita ce tabbatar da dorewar doka da oda a cikin al’umma a samu dorewar zaman lafiya a kare rayuwa da mutuncinsu da kuma kare diyaucin ita kanta kasar.
Daga wannan doguwar gabatarwa ce, ya zuba wa gwamnatin kirari da cewa: “Gwamnati ikon Allah. Gwamnati ba ki asara, gwamnati sarkin iko, mai karyawa a gaba ko ba gaba. Gwamnati baiwar al’umma, mai hidima da hadama, mai kamu da saki, mai doka da oda, mai rarrashi da damka…”
Ya yi bayanin irin jawaban da shugabanninsu suka yi masu, inda a karshe aka yi masu kuri’a don fitar da dayansu wanda zai zama mahaukacin da gangan da zai yi aikin gano wani da ake zargin yana yin wasu abubuwan da suke barazana ga kasa.
Kwatsam! Sai kuri’ar ta fada kan Baba Zube, aka sallami saura shi kuma aka zaunar da shi aka yi masa bayanin karfafa gwiwa da yadda ake so ya gudanar da aikin.
Daga shafi na 11 zuwa na 18, a karkashin labari mai kanun: “Iya gani, iya kyalewa…” ya yi bayanin yadda ya zama mahaukacin da gangan din don gudanar da aikin bankado wancan mutumin da ake zargin yana fakewa da sayar da tsofaffin jaridu da sauran abubuwa, yana sayar da wiwi da safarar makamai, to amma da yake a gefe yana sayar wa manyan gari magungunan karfin maza. Hakan ya sa da an kama shi, sai manyan garin su yi ruwa da tsaki su kwato shi. Haka Baba Zube ya yi amfani da shigar hauka har ya tare a kasuwar a karshe ya gano sirrin ta’asar da wannan dan kasuwa yake aikatawa hukuma ta kama shi, su kuma masu karbo shi daga hukuma da sun je suka ji abubuwan da yake yi sai su cika wa rigunansu iska su sulale.
Sai labari na gaba mai suna: “Dan Dugajin Jami’a,” na wani dalibi takadari da ya addabi Jami’ar Benin. Dalibin ya shahara da Sara-suka da daba da rashin tausayi ga ‘yan uwansa dalibai da ma’aikata da ‘yan kasuwar da ke cikin jami’ar da jama’ar gari. Da koke-koke suka yi yawa a kansa ne aka tura batun ga hedikwatar Hukumar Tsaro ta Kasa, (FSS), aka tura su Baba Zube su uku, aka yi masu katin shaida na dalibai, suka shiga aikin gano, hakikanin abin da ke faruwa game da wannan takadarin dalibi.
Daga farko sun dauka matsalar ta shafi fataucin miyagun kwayoyi ne ko makamai ga miyagu. Amma da suka ci gaba da bibiya, sai suka fahimci, masu fakewa da wannan coci da kuma Babban Padan, suna da wani mugun shiri ne na ci gaba da kokarin ballewa daga Nijeriya. Kuma ba za su yi haka ba, sai sun nakasa yankin Arewa da ya tsole musu ido, ta hanyar amfani da matsalar Boko Haram da ‘yan bindigar daji wato bandits.
Hakika marubucin wannan littafi ya haska wa makaranta yadda gwamnati ke amfani da jami’an tsaro wajen dakile duk wata barazana da ka iya wargaza kasa ko kawo fitinar da za ta cutar da al’umma. Duk da cewa kirkira ce, amma yadda ya tsara littafin kai ka ce, abu ne da ya faru da gaske.
Da za a dauki manyan labaran a yi fina-finai da su tabbas da sakon zai fi isa ga jama’a musamman a wannan lokaci da mutane suka fi karkata ga kallon fina-finai fiye da karatu.
A wannan dab’i an yi kokarin range kura-kuran da aka samu a bangaren ka’idojin rubutun Hausa. Sai dai an ci gaba da samun matsalar Bausanci, wato matsalar mayar da jinsin made namiji ko namiji mace. Sannan akwai wurare da dama da aka hade kalmomin da ya wajaba a raba su, ko aka raba wadanda ya wajaba a hade su. Sai kuma rubuta farkon wasu kalmomin da babban baki maimakon karami. Muna fata za a gyara Wadannan kura-kuran kafin fitowar littafin zuwa kasuwa.
Sun yi ta bibiyar abubuwan da yake yi, da suka ga munin barnar da yake yi, kuma babu alamar zai shiru a gaba, sai suka dana masa tarkon da a karshe suka yi masa illar da ya sheka barzahu ba tare da wani ya sani ba.
Daga shafi na 30 zuwa na 72 kuwa labarin wani gari ne da ‘yan bindiga suka addaba a Jihar Katsina, inda wani mutum mai suna Malam Dendo wanda dan garin Kiyawa ne a Jihar Jigawa, kuma ma’aikacin Hukumar Tsaron cikin gida, da ke hutunsa na yin ritaya daga aiki aka gayyato shi cewa ya je wani gari mai suna Sasagu a Karamar Hukumar Kankara, don magance matsalar ‘yan bindiga da suka addabe su. Da ya je garin sai ya nuna shi dan asalin garin ne da aka haife shi a wajen garin, ya girma har ya yi aikin gwamnati ya yi ritaya, kuma mahaifinsa bai nuna masa garin ba, balle ya san danginsa ba, duk da haka yanzu ya dawo gida tare da matarsa mai suna Ladi,. Wannan abin ya faru ne a daidai lokacin da wasu mutanen garin ke hijira saboda hare-haren ‘yan bindiga. Bayan an kai wa garin hari sau biyu an yi guje-guje tare da shi, sai ya shaida wa hakimin garin ya tara masa mutanensa akwai shawarwarin da zai bayar kan lamarin. A nan ne ya yi masu huduba ya tayar musu da tsimi, ya tunatar da su jarumtar iyaye da kakanninsu, ya nuna musu bai kamata su mika wuya ga ‘yan bindigar ba. Su ma su yunkura su tunkare su har su murkushe su. Ya gayyato abokinsa Baba Zube suka tsara yadda za su bullo wa lamarin. An fafata sau uku, biyu na farko na dakile hare-haren ‘yan bindigar ne, na karshe kuma Malam Dendo ne ya jagoranci kai hari har matsugunin ‘yan bindigar. A Dylan hare-haren ana samun nasara kan ‘yan bindigar, inda a na karshe aka murkushe su, sai dai Malam Dendo ya yi shahada. Kuma ganin haka Hakimin Sasagu ya sauya wa garin suna daga Sasagu zuwa Garin Malam Dendo.
Daga shafi na73 zuwa na 98, labarin wani mai suna Dan Dugajin Delta ne. Shi kuma ya kafa wata kungiya ce ta matasan kabilunsu biyu da sunan yaki don kwato musu ‘yanci daga gwamnati da kamfanonin man fetur. Shi ma Baba Zube ne aka tura da mutum biyu don bibiya da daukar matakin magance lamarin. Sun yi ta gudanar da aikinsu, kuma don magance tsoma bakin manyan gari, aka cire hannun Daraktan Hukumar Tsaro ta FSS da ke jihar. A karshe wanda ake zargin ya shiga hannu, jami’an tsaron suka dinga bincikarsa har ya fallasa masu ingiza su da masu hannu da masu karkatar da kudaden da gwamnati da kamfanonin mai suke bayarwa don alkinta muhallinsu. A karshe da Baba Zube ya lura zai iya kintsuwa ya zama mutum nagari, sai ya shawarce shi ya dan bar kasar nan, ya koma wata kasa ya rika kasuwanci. Hakan aka yi, bayan wani lokaci sai ga shi ya zama hamshakin mai kudi. A karshe har ya dawo Nijeriya ya zama dan Majalisar Wakilai.
Daga shafi na 99 zuwa na 109, a labari mai kanun, “Mata masu gari,” Baba Zube ya yi wa sababbin jami’an tsaron bayani ne kan irin matan da suka kamata su aura domin su ji dadin gudanar da aikinsu, har su samu nasara.
Sai kuma ya nusar da su kan wasu ka’idojin rayuwa daga shafi na 110 zuwa na 118. Ya jero wasu abubuwan kiyayewa da na aikatawa da na gujewa.
Sai labari na karshe mai kanun “Tawagar Babban Padan Ikilisiyya.” A wannan labari ya fito da wani mugun shiri ne da wasu suke yi don wargaza kasa. Wato masu shirin kafa kasar Biyafara.
Shi wancan Babban Pada na da hedikwatar Ikilisiyyarsa a kasar Ghana ce, su kuma masu fakewa da cocinsa don yunkurin wargaza kasa ‘yan Nijeriya ne da suka fito daga kabila daya a yankin Kudu maso Gabas. Jami’an tsaro na farin kaya a karkashin Baba Zube sun yi ta bibiyar take-taken wadannan mutane da sauran wakilansu. A wannan bangare an fi fito da irin yadda miyagu suke amfani da juya harshe ko kalma su fadi magana akasin abin da mai sauraro ya sani, to amma su jami’an tsaro ana koyar da su irin wadannan kalmomi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp