Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi Ta Kasa NDLEA sun damke wata motar haya bas dauke da jabun kudi Naira miliyan 3.2 mallakar wasu mutum uku: Fabour Peter mai ciki wata takwas mai shekaru 24; Esther Adukwu, mai shekaru 27 da Ochigbo Michael, mai shekaru 39, wadanda aka kama a tashar mota ta Jabi da ke Abuja, a wani sumame da aka kai ranar Talata, 9 ga watan Afrilu, 2024, biyo bayan kama wasu kudaden na jabun Naira a Lokoja, jihar Kogi.
Hakan ta faru ne a daidai lokacin da jami’an NDLEA tare da hadin gwiwar rundunar sojojin ruwan Nijeriya da ke Lugard Base a Lokoja suka kama wani Aliyu Lawal dan shekara 37 a hanyar Lokoja zuwa Abuja ranar Litinin, tare da kwato dauri 620 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 310 daga gare shi, yayin da jami’an NDLEA ta kama Jama Obodo, mai shekaru 44, da buhu 10 na wannan taba mai nauyin kilogiram 98 a kan titin Okene zuwa Lokoja-Abuja a cikin wata motar haya bas da ta taso daga Ilesha, jihar Osun ta hanyar zuwa Jihar Taraba a Afrilu.
- Wata Kungiya Ta Shirya Samar Da Gidaje Masu Saukin Kudi 400,000 A Nijeriya
- Jihar Benuwai Ta Bankado Mutum 35 Masu Yi Wa Sirin Tattara Harajinta Zagon-Kasa
A Jihar Kuros Riba, an kama wata bazawara mai shekaru 40 da haihuwa kuma mahaifiyar ‘ya’ya biyu, Misis Theodora a Bassey Edom, Calabar, sannan jami’an sun kama wata mata mai shekaru 40 da haihuwa a garin Bassey Edom da ke Calabar bisa laifin hadawa gami da sayar da wani sabon sinadari mai saurin kisa, NPS, a cikin gida. mai suna ‘Combine’, wato a hda gami da cakuda nau’ikan cannabis daban-daban da opioids wadanda aka jika a cikin danyen sinadarin Gin.
A lokacin da aka kama ta, an kwato lita 18 na sinadari mai hatsarin gaske a cikin bokitin fenti.
Yayin dake amsa tambayoyi, ta yi ikirarin cewa ta fara samar da wadannan haramtattun magunguna ne da rarrabawa a watan Oktoban 2023. Wani wanda ake zargi, Godwin Okon Samuel, mai shekaru 48, an kama shi a unguwar Essit Ebum da ke Calabar da kilogiram 39.4 na tabar wiwi a ranar Talata, 9 ga Afrilu.
Yayin da aka kama wasu mutum biyu: Sani Mohammed, mai shekaru 43, da Christopher Eze, mai shekaru 64 a unguwar Sabon Gari dake Kano a ranar Talata, 9 ga watan Afrilu, tare da kwato kwayoyi na opioid 900,000 daga hannunsu, jami’an NDLEA da ke sintiri a hanyar Owerri-Onitsha, Jihar Imo, a ranar Juma’a, 12 ga Afrilu, ta kama wata babbar motar daukar kaya mai lamba JGB 403DB, inda ta gano cannabis 230 na Satiba mai nauyin kilogiram 119 da aka boye a karkashin kayayyakin gida, bayan tsananta bincike.
An kama akalla kilogiram 252 na tabar wiwi yayin wani samame da aka kai dajin Ijesa Isu, Jihar Ekiti a ranar Asabar 13 ga watan Afrilu yayin da wasu mutum hudu: Adamu Umar, mai shekaru 39; Abdullahi A Gimba, mai shekaru 27; da kuma Julius Uduakhomu, mai shekaru 28; an kama Micheal Sunday, mai shekaru 24, suna lodin kilogiram 40 na kaya maye a dakin da aka ajiye injin wata motar gas a kauyen Agho dake yankin Owan ta Gabas ta Jihar Edo.
An kuma gano babura biyu da aka yi amfani da su wajen kai kayan zuwa inda motar iskar gas din ta nufa.
A Jihar Ogun, an kama wani da ake zargi mai suna Ismaila Ogun a ranar Juma’a, 12 ga watan Afrilu da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 79 a Imeko, yayin da aka kama wani matashi mai suna Friday Abah mai shekaru 18 da kilogiram 410 na irin wannan taba a lokacin da jami’an NDLEA suka kai farmaki sansanin Obatedo, dajin Itaogbolu, a Karamar Hukumar Akure ta Arewa, Jihar Ondo.
Wata sanarwa da Daraktan Yada labarai da bayar da shawarwari Femi Babafemi,ya fitar a shalkwatar hukumar ta NDLEA da ke Abuja, ya ce da irin wannan himma, tare da ba da umarni daban-daban na hukumar a fadin kasar nan, jami’an sun ci gaba da fafutukar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi.
Wasu daga cikin ayukan sun hada da: Lakcar wayar da kan dalibai da ma’aikatan Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Gboko, a Gboko, Jihar Binuwai, wato WADA; Hafsoshin soji da mutum 15 na ‘Engineering Field Regiment Nigerian Army’, Topo, Badagry Lagos; mahautar nama ta Odo Eran, Osogbo, Jihar Osun kai ziyarar gami da ba da shawarwari ga Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, da dai sauransu.
Yayin da yake yaba wa Hafsoshi da jami’an Kogi, Cross Riber, Ondo, Ekiti, Ogun, Imo, Kano, da Edo na hukumar kwamandojin hukumar bisa bajintar da suka yi wajen rage yawan shan miyagun kwayoyi, Babban Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya), ya kuma yaba musu da takwarorinsu na dukkan bangarorin kasar nan kan yadda suka karfafa lakcocinsu na ‘WADA’, da nufin rage sha’awar shan miyagun kwayoyi.