Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya), ya bayyana cewa hukumar ta cafke mutane sama da 18,500 da ake zargi da ta’ammuli da miyagun ƙwayoyi a bara.
Hakazalika, Marwa ya ce NDLEA ta ƙwace haramtattun ƙwayoyi masu nauyin kilogiram miliyan 2 da dubu 600 a shekarar.
- Awannin Da Sallamarsu A Matsayin Kwamishinoni, Gwamnan Bauchi Ya Naɗa 3 A Matsayin Mashawarta
- Ana Kara Zuba Jarin Waje A Kasar Sin A Sabuwar Shekara
Ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ake ƙaddamar da sabon ofishin hukumar da gwamnatin Amurka ta gina a Jihar Legas a ranar Talata.
Sabon ofishin, wanda za a riƙa amfani da shi wajen tattara da tantance hujjoji kan muggan ƙwayoyi, ya samu yabo daga Marwa, wanda ya gode wa gwamnatin Amurka saboda goyon bayan da ta ke bai wa NDLEA wajen yaƙi da safarar ƙwayoyi.
“Na gode wa Amurka bisa wannan ofishin da zai taimaka wajen tabbatar da shari’ar masu laifukan da suka shafi ƙwayoyi,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa duk da wannan nasarar, akwai sauran aiki a gaba domin kawo ƙarshen matsalar shaye-shaye da safarar ƙwayoyi a Nijeriya.
Marwa, ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka cafke a shekarar, an gurfanar da 3,250 a kotu, ciki har da gaggan masu safarar ƙwayoyi guda 10.
A gefe guda, ya ce hukumar ta yi nasarar sauya wa mutane sama da 8,200 tunani tare da raba su da shaye-shaye.
Marwa ya ce NDLEA za ta ci gaba da jajircewa wajen yaƙi da matsalar har sai ta rage yawan masu safarar ƙwayoyi da masu shan su a Nijeriya.