Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ta damke wata mai suna Opoola Mujidat, da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar Oman, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a jihar Legas.
An kama ta ne bayan hukumar ta kama wasu fasinjoji biyu da ke tafiya Oman a ranar Litinin, 11 ga Yuli.
- Da Dumi-Dumi: Tsohuwar Shugabar Mata Ta APC, Kemi Nelson, Ta Rasu
- Sabon Gwamnan Osun: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Ademola Adeleke
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi, ta ce an kama fasinjojin biyu, Raji Babatunde Kazeem da Akinbobola Omoniyi kafin su hau jirgi.
“Fasinjojin, Raji Babatunde Kazeem da Akinbobola Omoniyi, suna tafiya tare zuwa kasar Oman da ke Gabas ta Tsakiya a cikin jirgin kasar Habasha a ranar Litinin 11 ga watan Yulin shekarar na ta 2022 inda jami’an NDLEA suka tare su a filin jirgin.
“A binciken da aka yi a cikin jakunkunansu, an gano kullin tabar wiwi da aka boye a cikin wata jaka dauke da kayan abinci, wanda Kazeem ke dauke da ita.”
“Nan da nan Kazeem da Omoniyi suka sanar da jami’an yaki da miyagun kwayoyi cewa Mujidat da ke kusa da wurin ce ta ba su jakar da ke dauke da haramtattun kayan a filin jirgin, nan take kuma aka kama ta.”
A cewar sanarwar, Mujidat ta yi ikirari cewa ta kawo kayan ne da nufin fasinjojin biyu su bawa mijinta da ke can a kasar Oman din.