Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ta kama kilo 588 na miyagun kwayoyi tare da lalata gonakin wiwi masu girman hekta shida a jihar Adamawa.
Kwamandan hukumar a jihar, Barr. Aliyu Abubakar, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Yola, inda ya ce gonakin wiwin sun shigo hannu ne a wani sumame da aka kai a ƙauyen Mijilu na ƙaramar hukumar Mubi ta Arewa. Ya ce jami’an hukumar sun kuma cafke mutum biyar da ake zargi da hannu a badaƙalar.
- Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 14 A Borno Da Adamawa, Sun Ƙwato Makamai
- ‘Yansanda Sun Ceto Yara 5 Da Aka Sace A Adamawa
A cewarsa, hukumar ta kama mutum 58 da ake zargi da fataucin miyagun ƙwayoyi, inda aka ƙwato kilo 366.8 na wiwi, kilo 209.8 na wasu ƙwayoyi masu sa maye, da kilo 11.6 na ƙwayar methamphetamine da makamantansu. Haka kuma, an cafke wani fitaccen dillalin kwayoyi mai suna Suleiman Mohammed, wanda aka ce tsohon ɗan fursuna ne, tare da wani mutum guda da kilo 40 na wiwi aka karɓo daga hannunsu.
Abubakar ya ce a watan Satumba an kuma ƙwace wata mota ƙirar Honda mai lambar GUY-12AA (Adamawa), ɗauke da buhunan wiwi fiye da 500 daga Akure, jihar Ondo zuwa Mubi. Haka nan, a wata babbar nasara ta Operation Farauta, hukumar ta kama kilo 131 na ƙwayoyi masu sa maye tare da kwace wata Toyota Sienna da aka yi amfani da ita wajen jigilar kayan.
NDLEA ta ce a ɓangaren rage buƙatar miyagun kwayoyi, ta gudanar da shawarwari da kuma horas da matasa 70 masu fama da shaye-shaye, yawancinsu na tsakanin shekaru 18 zuwa 43. Haka kuma, hukumar ta gudanar da gwajin jinin ga mutane 25 domin tabbatar da cewa masu shiga ayyukan gwamnati ko makarantu ba su karkata ga amfani da miyagun kwayoyi ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp