Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, a Jihar Kuros Riba ta kama wani malamin makaranta mai shekaru 52, Onun Ikoli, da matarsa, Itam Onun, bayan an gano buhunan wiwi 360 masu nauyin tan 4.706 a gidansu da ke yankin karamar hukumar Yakurr.
Kwamandan NDLEA na Jihar, John Anteyi, ya bayyana nasarar ga manema labarai a ranar Laraba a Calabar.
Anteyi ya ce, ma’auratan sun yi ikirarin cewa, haramtattun kayayyakin ba mallakinsu ba ne, na wani ɗan haya ne, kuma ya arce yayin da ya hangi zuwan jami’an hukumar ta NDLEA.
Don haka, Anteyi ya bayyana cewa, tuni rundunarsa ta fara bincike don cafke duk wanda ke da hannu kan mallakar haramtattun kayayyakin.














