Daga Muhammad Awwal Umar,
Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello, ya bayyana cewar, hade dokokin samun kudaden shiga tsakanin jiha da kananan hukumomi zai rage yaduwar rashawa kuma ya taimaka wajen karin kudaden shigar jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake bude taron horarwa da karawa juna sani ta hanyar hade dokar tara kudaden shiga na shekarar 2020 wanda ya gudana a gidan gwamnatin da ke minna.
Gwamnan ya bayyana cewar taron karawa juna sani yazo akan kari a lokacin da jiha ke fuskantar matsalolin shiga akwai bukatar karin samun hanyoyin kudaden shiga ta hanyar hade masu karban kudaden shigar a jihar.
“Ta hanyar hade masu karban kudaden shigar, za mu iya samun biliyan biyu zuwa uku a wata dan cika gurbin kudaden da muke hasara daga aljihun gwamnatin tarayya dan samun yin ayyukan raya kasa a jihar,” a cewarsa.
Gwamnan ya bukaci ma’aikatan da ke karban haraji da su kara baza komarsu da kaucewa sake karban kudi a hannun wadanda suka riga suka biya tun farko.
Ya bayyana cewar rashin tsaro na daga cikin abinda ke janyowa karban haraji koma baya a jihar musamman a wasu yankunan kananan hukumomi ya ba su tabbacin komai zai daidaita.
Gwamnan ya sake tabbatar da cewar hade karban kudaden shiga waje daya zai taimaka wajen samun gudanar da ayyukan da ya rataya a wuyan su.
Ya ce, jihar za ta iya tsayawa da kafarta ta hanyar kudaden da ke shigo ma ta na cikin gida ba tare da dogaro akan kudaden da gwamnatin tarayya ke ba ta ba.
Gwamnan ya bayyana cewar noma da yawon bude ido da ma’adanan kasa suna daga cikin abubuwan da ke bunkasa tattalin arziki, ya ce in har za mu mayar da hankali sosai, za mu iya samun kudade masu yawa a jihar nan.
Kwamishinan shari’a, Mai shari’a Barista Nasara Dan-Mallam ya bayyana cewar kan kudaden shiga, idan dokar ta tabbata, zai taimaka wajen bunkasa kudaden shigar jihar.
Shugaban riko na hukumar tara kudaden shigar jihar, Ahmed Garba Gunna ya ce gabatar da wannan dubarar manufa ce ta daga karin kudaden shigar jiha da kananan hukumomi.
Garba Gunna ya ce tun darewar wannan gwamnatin akan wannan kujerar, kudaden shigar cikin gida da jihar ke samu ke karuwa a duk shekara, ya bada tabbacin zai kara mayar da hankali wajen samarwa jihar kudaden shiga ta hanyar anfani da fasahar zamani wajen dakile rashawa dan samun kudade masu yawa.
Shugaban rikon, ya janyo hankalin masu biyan haraji akan tsoron da suke ji kan kudaden da suke biya, da cewar ba zasu biya haraji sau biyu ba.
Da yake bayani a taron karawa juna sanin, kwamishinan kudin jiha, Abubakar Zakari ya ce taron karawa juna sanin wani yunkuri ne na gwamnatin jiha da zai taimaka wajen samun karin kudaden harajin da jihar ke samu, ya kara da cewar wannan zai samar wani sabon tsarin da zai taimakawa jihar samun kudaden shiga.