Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da Hezbollah yayin wata tattaunawar tsaro tare da jami’an Isra’ila a jiya Lahadi.
Duk da haka, Isra’ila tana da shakku kan wasu bayanai na yarjejeniyar da za a isar wa gwamnatin Lebanon a yau Litinin. Har yanzu ana tattaunawa kan waɗannan batutuwan, kuma yarjejeniyar ba za ta zama cikakkiya ba har sai an warware dukkan matsalolin.
- Wakilin Sin Ya Bukaci Isra’ila Da Ta Dakatar Da Amfani Da Agajin Jin Kai A Gaza A Matsayin Hanyar Cimma Bukatar Kashin Kai
- Kin Amincewa Da Kudurin Tsagaita Bude Wuta A Gaza Da Amurka Ta Yi Ya Kara Nuna Rashin Mutunci Da Adalcinta
Har yanzu ana samun musayar wuta tsakanin Isra’ila da Hezbollah, wanda zai iya kawo cikas ga yarjejeniyar, in ji wani rahoton CNN. A kwanakin baya, Hezbollah tana nazarin wani shirin tsagaita wuta na tsawon kwanaki 60 da Amurka ke mara wa baya, wanda ake fatan zai zama tushen tsagaita wuta na dindindin.
Tun daga tsakiyar watan Satumba, Isra’ila ta ƙaddamar da babban hari a Lebanon bayan hare-haren iyaka da suka faro tun 8 ga Oktoba na bara, lokacin da Hezbollah ta kai hari a kan wani yanki da ake ta
Isra’ila a matsayin nuna goyon baya ga Hamas da Falasdinawa a Gaza. Tun daga lokacin, Isra’ila ta fara farmaki ta kasa, ta kashe manyan shugabannin Hezbollah, ciki har da Hassan Nasrallah, daya daga cikin ƙusoshinta, tare da jikkata dubban mutane har da fararen hula.
Tuni dai cikin makon nan kotun hukunta masu manyan laifuka ta duniya ta bayar da umarnin kama shi domin fuskantar hukunci sakamakon laifuffukan yaki da ya aikata kan Falasɗinawa.