Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yanke hulda tsakaninta da Nijeriya da Togo da Amurka da kuma Faransa bayan ECOWAS ta tura tawaga don tattaunawa da sojojin da suka yi wa shugaba Bazoum juyin mulki.
A wani jawabi da ya yi ta kafar yada labaran Nijar, jagoran juyin mulkin, Kanar Amadou Abdramane ne, ya sanar da matakin da ma wasu matakan da suka dauka.
- Abubuwan Da Suka Gudana A Zanga-zangar Cire Tallafin Mai
- Gwamnatin Tarayya Ta Rufe Iyakokin Nijeriya Da Nijar
Ya ce “Mun kawo karshen duk wata huldar jakadanci da Nijeriya da Faransa da Togo da kuma Amurka. Duk wata matsaya da aka cimma a baya ta rushe.”
Tawagar da ECOWAS ta tura don tattaunawa da sojojin Nijar a karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar, ta gana da wasu daga cikin sojojin a ranar Alhamis amma ba a cimma matsaya ba.
Manyan hafsoshin sojin ECOWAS sun kammala wani taro a Abuja, inda suka tattauna yiyuwar faukar matakin soji a kan Nijar idan sasanci ya gagara.
A ranar Larabar da ta gabata ne sojojin fadar shugaban kasar Nijar suka hambarrar da gwamnatin shugaba Bazoum.