Gwamnatin Nijeriya da masarautar Saudiyya sun sanya hannun yarjejeniya domin bunkasa hadin guiwar fasaha, bangaren musayar fasahar sadarwa tsakanin kasashen biyu a bangaren mai da iskar gas.
Da ya ke bayani kan gagarumin matakin, a wata sanarwa, ministan albarkatun Mai, ya ce, hadin guiwar za ta taimaka wajen kara samar da hadin guiwa da fahimtar juna a tsakanin kasashen biyu dangane da bangaren samar da mai.
- Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Ngaski Ya Samu ‘Yanci Bayan Shafe Makonni 3 A Hannun ‘Yan Bindiga
- Za A Samar Wa ‘Yan Nijeriya Gida 80,000 Cikin Shekara 4
Sanarwar dauke da sanya hannun Nneamaka Okafor, kakakin ministan mai Heineken Lokpobiri, ya ce, ministan ya wakilci Nijeriya a wajen bikin sanya hannun, inda ministan makamashi na kasar Saudiyya ya wakilci sarki Abdulaziz bin Salman, yayin rattaba hannun.
Sanya hannun fahimtar junan (MoU), a cewar Lokpobiri, za ta taimaka sosai wa Nijeriya wajen kyautata fitar da mai da kuma fasaha hadi da bangaren makamashi.
Sanya hannun wacce ke da manufar kara kyautata alaka da juna da manufar samar da tsarin bunkasa harkokin mai da gas a kasashen biyu.
Babban manufar sanya hannun sun hada da taimaka wa juna wajen musayar bayanai, musayar raayin fasaha ta hanyar da za a samu kafa da aza yanayin fahimta da kasashen biyu za su amfani junansu, sanarwar ta kara.
Tare da Saudiyya za mu samu damar bunkasa fasahohi a bangaren hako mai da iskar gas, Nijeriya za ta samu tagomashi sosai da musayar ilimi.
Ta fuskacin musayar fasaha, Nijeriya za ta samu damar da za ta kyautata harkokin makamashi da zai taimaka sosai wajen kara bunkasa hanyoyin da ake bi wajen fitar da mai da kuma shiga tsarin duniya.
Kazalika, amincewar yarjejeniyar ana sa ran zai janyo hankalin masu zuba hannun jari kai tsaye da su zo Nijeriya domin zuba hannun jari a bangaren mai da iskar gas. Kasar Saudiyya da take taka gagarumin rawa a kasuwar makamashi na duniya, ta na da gagarumin rawar da za ta taka wajen ci gaban zuba jari a Nijeriya.
Wannan, zai taimaka matuka gaya wajen cigaban tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma bunkasa shimfida ayyukan raya kasa. Kuma, wannan matakin zai taimaka sosai wajen kyautata kasuwancin mai a Nijeriya, sannan, bangarorin cigaban tattalin arziki da dama za su samu damar habaka, a cewar ministan.
Bugu da kari, tsarin fahimtar junan, zai kuma taimaka wajen kyautata hadin guiwar fasahohi da na harkokin kudi.