Ministan Wasanni da Nishaɗi na Ghana, Kofi Adams, ya bayyana cewa Ghana za ta iya yin haɗin gwuiwa da Nijeriya da Cote d’Ivoire wajen karɓar baƙuncin gasar cin kofin duniya na FIFA a nan gaba. Adams ya yi wannan jawabi ne bayan FIFA ta amince da cewa ƙasashe da dama za su iya haɗin gwuiwa su karɓi gasar a lokaci guda.
Adams ya ce, “Ghana, tare da Nijeriya da Cote d’Ivoire, waɗanda sun samu ƙwarewa wajen shirya gasar AFCON, za su iya karɓar baƙuncin gasar cin kofin Duniya nan gaba. Muna buƙatar shirye-shirye masu kyau daga gwamnati domin tabbatar da wannan mafarki.”
Ya ƙara da cewa shirye-shiryen da aka yi a baya wajen ɗaukar nauyin gasanin Afrika a ƙasashen ya basu damar nuna ƙwarewa da ƙarfin iya gudanar da manyan gasanni, kuma hakan na iya zama hujja ta nuna cancantar ɗaukar nauyin gasar duniya.
Ghana ta karɓi baƙuncin babban taron wasanni na ƙarshe a 2024, yayin da Cote d’Ivoire ta ɗauki nauyin gasar cin kofin Afrika na 2023 inda ta doke Nijeriya a wasan ƙarshe. Wannan na nuna cewa haɗin gwuiwar ƙasashen na iya samar da nasarori a matakin duniya.














