Nijeriya ta gabatar da bukatarta na neman cikakken wakilci na didindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
Ta ce, ta bayar da gagarumin gudunmawa har sau akalla 41 a yayin gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya a fadin duniya, kuma ta tura dakarun ta sojin Nijeriya su sama da 200,000 a ayyukan Majalisar Dinkin Duniya, don haka ta ce, ta cancanci a ba ta kujerar dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
- Jihar Kano Ta Musanta Zargin Karɓar Bashin Biliyan 177 Daga Faransa
- An Kashe Jagororin ‘Yan Bindiga, Sani Black Da Kachalla Makore A Zamfara
Ministan tsaron Nijeriya, Mohammed Badaru, shi ne ya nuna wannan bukatar a yayin da yake jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 da ya gudana a New York na Amurka ranar Lahadi.
“Nijeriya na kira ga yin garambawul ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ta yadda za a bai wa Afrika wakilci na dindindin domin shigo da kowani bangare cikin sha’anin wanzar da zaman lafiya da tsaro a fadin duniya.”
Badaru wanda ke magana a wajen taron tattauna yadda za a shigo da kowani bangare wajen kyautata zaman lafiya da tsaro a duniya. Ya ce muddin aka amince da bukatar nasu, za a kara samun wakilci wajen kyautata lamuran tsaro a Nahiyar Afirka.
Kwamitin tsaro dai na daga cikin muhimman bangarori 6 da suka hada Majalisar Dinkin Duniya. Yana da mambobin dindindin guda 15 da suke da alhakkin wanzar da zaman lafiya da tsaro a duniya, bayar da shawarar sabbin mambobin ga babban taron majalisar, amincewa da sauye-sauyen ga yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.
An kafa kwamitin tsaron da nufin wanzar da ayyukan zaman lafiya da sanya takunkumi da kula da ayyukan sojoji.
A taron, ministan tsaron ya ce, “Nijeriya ta himmatu wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya, tun lokacin da ta fara tura dakarunta na soji zuwa Congo a 1960, domin kwantar da tarzoma.
“Zuwa yau, Nijeriya ta ba da gudunmawarta wajen wanzar da zaman lafiya har sau 41 a ayyukan wanzar da zaman lafiya a fadin duniya, tare da amfani da sojoji sama da 200,000 a ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.
“A ayyukan shiyya kuwa, Nijeriya ta taka rawa wajen gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a Cote d’Iboire, Guinea-Bissau, Gambia, Liberia, Mali, Sudan da Sierra Leone, da sauran kasashen, kuma ta bayar da gudunmawar kudade, kayan aiki, kwararrun soji, da hakan ya kaita ga zama kasa da ta fi kowace kasa bayar da gudunmawar soji da ‘yansanda a ayyukan Majalisar Dinkin Duniya.”
Shi kuma a nasa bangaren, ministan kula da harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar, ya yi kira ne ga shugabannin kasashen duniya da su bayar da kula wajen daurewar ci gaba, musamman a Nahiyar Afirka.
Tuggar ya bukaci kasashen da suka ci gaba da cika alkawuran da suka dauka na tallafa wa yankin Kudancin Duniya, yana mai jaddada cewa rashin cimma manufofin muradin karni ya kamata a tsawaita wa’adin shekarar 2030.
Ya kuma ba da shawarar sake yin kwaskwarima ga tsarin hada-hadar kudi na kasa da kasa domin tabbatar da gaskiya da rikon amana, tare da daukar kwararan matakai na yafe basussuka domin rage matsin tattalin arziki da kasashen Afirka ke fuskanta.