Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ta biya dukkanin kuɗaɗen tallafin karatu na ɗaliban Nijeriya da ke karatu a ƙasashen waje a ƙarƙashin shirin ilimi na (BEA) har zuwa watan Disamba 2024.
A cikin sanarwar da Daraktan hulɗa da jama’a na ma’aikatar ilimi, Boriowo Folasade ta fitar, ta bayyana cewa ma’aikatar ta amince da cewa sauye-sauyen farashin musayar kuɗin ƙasashen waje sun haifar da ƙarancin kuɗaɗen da aka tura.
- Fiye Da Dalibai 4,200 Suka Amfana Da Tallafin Ilimi Na Sanata Solomon Adeola
- Minista Ya Gargaɗi Jami’an Gwamnati Kan Rashin Sanin Ilimin Tantance Ingantattun Labarai
Ta ƙara da cewa, Ministan Ilimi ya nema ƙarin kuɗin don rufe wannan giɓin da kuma tabbatar da cikakken biyan haƙƙoƙin dukkan ɗaliban da abin ya shafa.
Ma’aikatar Ilimi ta tabbatar wa da dukkan masu ruwa da tsaki da cewa tana ci gaba da aiki tukuru don tallafawa ɗaliban Nijeriya a ƙasashen waje, kuma tana aiki tuƙuru don cika dukkan sauke alhakin da ke ƙarƙashin shirin BEA kan lokaci.
Shirin BEA, wanda ya samo asali daga dangantakar diplomasiyya da haɗin gwuiwa, yana ba wa ɗaliban Nijeriya damar ci gaba da karatu a ƙasashe kamar China, Rasha, Algeria, Hungary, Morocco, Egypt, da Serbia, inda ake ba su kyautar kuɗin makaranta, ko ayi musu rangwame, da kuɗin alawus na wata-wata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp