A ranar Talata ce, gwamnatin tarayya ta sake jaddada hana shigo da shinkafa a cikin kasar nan duk da bude iyakokin kasar. Shugaban hukumar Kwastan ta Nijeriya reshen Jihar Sakkwato da Zamfara, Mista Abdullahi Ma’aji shi ya bayyana haka a bakin iyakan Illela da ke Jihar Sakkwato wanda aka bude a makonnin da suka gabata.
An bayar da rahoton cewa, gwamnatin tarayya ta kara jadda hana shigowa ko fita da shinkafa ta Jihar Sakkwato, sakamakon sake bude iyakan Illela. Shi dai iyaka na Illela daga da iyaka ce tsakanin Nijeriya da kasar Jamhuriyar Nijar.
Ma’aji ya bayyana cewa, za su tabbatar da cewa sun tsaftace iyakar kasar nan daga haramtacciyar kasuwanci da gwamnati ta hana. Ya kara da cewa, an rufe iyakokin Nijeriya ne domin ya amfani ‘yan Nijeriya. Shugaban hukumar Kwaston ya ce, mafi yawancin ‘yan ta’adda suna amfani da iyakokin kasar nan wajen shigowa da haramtattukan kayayyaki wanda zai iya cutar da kasar nan. Ya ce, suna kokarin ta yadda za mu dakile lamarin. Ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi kokarin fahimci gwamnati tare da ba ta goyan baya wajen manufofin da take aiwatarwa, sannan ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su yi kokarin gudanar da kasuwancinsu bisa ka’idojin da gwamnati ta shardanta.
“Gwamnati tana samun nasarar cimma manufofin da ta aiwatar ne ta hanyar samun goyan bayan mutane da kuma mahimmiyar rawar da masu ruwa da tsaki suka taka,” in ji shi.
Wani mai fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare mai suna, Alhaji Ibrahim Milgoma ya bayyana cewa, lokacin da aka garkame iyakokin kasar nan, masu fitar da kayayyaki daga Nijeriya sun bi umurnin gwamnati duk da irin matsanancin rayuwar da suka fuskanta. Ya kara da cewa, haka kuma ma yanzu za mu yi kokarin bin dokokin da gwamnati ta tanada na sake bude iyakokin.
Shugaban kungiyar masu yin rijista na wakilan na kasashen ketare, Alhaji Aminu Dan’iya ya bayyana cewa, sun yi wa kamfanoni sama da 35 rijista a iyakar Illela a karkashin dokokin da gwamnati ta tanada.