Tawagar kwallon kafar Nijeriya ta Super Eagles, ta lallasa takwararta ta kasar Benin, da ci 3 da nema a filin wasa na Godswill Akpabio da ke birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.
Ana gab da tafiya hutun rabin lokaci ne, Ademola Lookman, ya jefa wa Nijeriya kwallonta ta farko a wasan kafin Viictor Osimhen ya kara ta biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
- Tallafin Lantarki Ga Asibitoci Da Manyan Makarantu Ka Iya Lakume Naira Biliyan 188
- 2027: Da Yiwuwar Atiku, Obi, Kwankwaso Su Yi Kawancen Siyasa – PDP
Lookman, ya jefa kwallonsa ta biyu kuma ta uku ga Nijeriya a minti na 80 wanda ya sa Nijeriya ta samu nasara a kan Benin da ci 3 da nema a wasan farko na gasar neman gurbin buga kofin nahiyar Afirika a shekarar 2025.
Talla