’Yan majalisa masu waklitar Nijeriya a kungiyar ECOWAS sun yi barazanar ficewa daga kungiyar saboda saba wasu ka’idojojin daukar aiki wanda haka bai yi wa Nijeriya dadi ba.
Wasu ‘yan majalisar dokokin kungiyar da suke wakiltar Nijeriya ne suka yi wa manema labarai bayani, sun bayyana cewa, a zaman majalisar na 2022 da aka yi a Abuja ranar 3 ga watan Yuli suka jagoranci yanke hukuncin zartas da dakatar daukkan shirin daukar ma’aikata a kungiyar.
- Buhari Ya Sake Shillawa Kasar Ghana Don Halartar Taron ECOWAS
- Matsalar Tsaro: An Kashe Mutane 14,500 A Yammacin Afirka Cikin Shekaru 4 – ECOWAS
Sun kara da cewa, shawarar ta biyo bayan rahotannin da aka samu na rashin bin ka’aida da rashin adalci da ke tattare da shirin daukar ma’aikatan, inda aka yanke hukuncin dakatar da shirin har sai an samu cikakken rahoto daga kwamitin binciken da aka kafa.
‘Yan majalisar daga Nijeriya sun kuma yi nuni da irin dumbin gudummawar kudade da Nijeriya ke bayarwa ga kungiyar duk kuwa da matsalolin da kasar ke fuskanta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp