Babban Sakataren Ma’aikatar Kasuwanci da Zuba Hannun Jari ta Tarayya, Ambasada Nura Rimi ya bayyana cewa; gwamnatin tarayya na shirin bunkasa noman Koko zuwa tan 500,000, daga nan zuwa shekarar 2025.
Domin kuwa a cewar ta Rimi, hakan zai taimaka wajen rubanya yawan Kokon daga tan 340,000 da aka noma a Nijeriya a shekarar 2022.
- Jarin Kai Tsaye Da Bai Shafi Hada-hadar Kudi Ba Da Sin Ta Zuba A Ketare A Rabin Farkon Bana Ya Kai Dala Biliyan 72.62
- Kotu Ta Umarci INEC Ta Tuhumi Gwamnoni Kan Rikice-rikicen Zaben 2023
Ambasadan ya sanar da hakan ne, a wata tattaunawa da aka yi, kan batun harkokin kasuwanci a Abuja; wanda Darakta a Ma’aikatar Kaura Irmiya ya wakilce shi.
Har ila yau, da yake yin karin haske a kan gudunmawar da noman Koko ke bayarwa wajen bunkasa fannin tattalin arzikin wannan kasa; Rami ya ce, Nijeriya ce kasa ta shida a duniya da ke noma Koko mai matukar yawa.
Kazalika, ya kara da cewa; fitar da Kokon da aka noma a fadin wannan kasa, ake kuma fitar da shi don sayarwa a kasuwar duniya; ya yi matukar karuwa.
Bugu da kari, ya kuma bayyana cewa; fitar da amfanin daga kasar nan zuwa kasuwar duniya, ya kara samar wa da kasar kudaden shiga masu dimbin yawa; wadanda suka kai kimanin kashi 50 cikin 100 a shekarar 2022.
Har wa yau, Rimi ya sanar da cewa; a shekarar 2023, an samu masu zuba hannun jari kai tsaye, wanda hakan ya yi sanadiyyar samun sama da dala biyan biyu a wannan kasa.
A cewar tasa, dabarun da aka samar na yin hadaka da kungiyoyin kasa da kasa, kamar irin na kungiyoyin noman Koko ta duniya (ICCO), da kuma gidauniyar kula da nomansa ta Afirka da sauran makamantansu; ya yi matukar taimakawa wajen samun gagarumar nasara da kuma ci gaba a wannan fannin matuka gaya.