Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTALIN ARZIKI

Nijeriya Za Ta Fita Daga Matsin Tattalin Arziki Zuwa Karshen 2020 – CBN

by Muhammad
November 26, 2020
in TATTALIN ARZIKI
2 min read
Karshen
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Yusuf Shuaibu

Bayan kammala taron kwamitin harkokin kudade na kwana biyu a ranar Talata, Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya yi tsammani cewa Nijeriya za ta fita daga cikin matsin tattalin arziki wanda ba ta taba fuskantan hakan ba tun bayan shekaru 33 a karshen wannan shekara. Duk da fuskantar matsalar hauhawar farashin kayayyaki da ake samu a Nijeriya, kwamitin harkokin kudaden ya kawo manufofin da aka samu nasarar rage na kashi 11.5, inda manufofin za su cigaba da aiki wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan, yayin da CBN yanke kokarin samun tallafin wasu bangarorin tattalin arziki domin kawo dauki wajen fita daga cikin matsin tattalin arzikin. Kwamitin ya jaddada cewa, za a samu bunkasa tattalin arziki a dan karamin lokaci da jimawa ba.

samndaads

Gwamnan CBN, Mista Godwin Emefiele ya bayyana cewa, akwai bayanai daga bangaren mahimman fannukan tattalin arziki da suka bayar da shawarwar wajen farfadowa daga cikin matsin tattalin arziki kafin kasarshen shekarar 2020, sakamakon ayyukan tattalin arzikin da suke gudanarwa. A cwarsa, ana tsammanin tattalin arzikin zai farfado kafin kasarshen shekarar 2020, yayin da za a magance hauhawar farashin kayayyaki kashin farkon shekarar 2021.

Mambobi guda 10 ne kacal daga cikin ‘yan kwamitin suka halarci taron kwamitin na baya a cikin shekarar 2020, haka kuma ana fatan kwamitin ya ci gaba da gudanar da wasu tsare-tsare da za su bayar da goyar baya wajen bunkasan tattalin arziki tare da kayyade rage ayyukan yi da bayar da dama ga ‘yan kasuwa masu zuba jari da kuma bayar da goyan bayan da ya dace ga bangaren lafiya, domin dakile matsalolin cutar Korona.

CBN ita take mahimmiyar rawa a duk lokacin da aka sami irin wannan lamari na matsin tattalin arziki wanda tuni ta fara rarraba wa kananan ‘yan kasuwa kudade wanda ya kai na naira biliyan 92.90, wanda kananan ‘yan kasuwa guda 24,702 suka amfana da wadannan kudade da samar da shirin noma wanda aka raba wa manoma guda 954,279 kudi na naira biliyan 164.91 da kuma bai wa magidanta guda 316,869 kudi na naira biliyan 149.21.

Kwamitin ya bayyana cewa, ya samu nasarar rage kudaden ruwa na bayar da bashi. A watan Oktobar shekarar 2020, an samu tallafin na basuka wanda ya kai na kashi 86.23 ga mutane guda miliyan daya da ke gudanar da harkokin kasuwanci. An samu bunkasar kashi 76.43 a watan Yulin shekarar 2019.

Kwamitin ya kara da cewa, kara bunkasa harkokin kudade ya taimaka wanda aka samu na kashi 15.5 na zabar kudin da ake gudanar da harkokin kasuwanci da na bashi wanda aka samu  kashi 5.73 da kuma kudaden da aka samu riba wanda suka kai na kashi 35.6 a cikin watan Oktobar shekarar 2020. Ya ci gaba da bayyana cewa, ana samun wannan nasarar ne sakamakon matakai da CBN tare da hadin gwiwar wannan kwamitin suka dauka na farfado da tattalin arziki a cikin kasar nan, kwamitin ya bukaci bankuna da su yi kokarin cike gurbin da aka samu wajen hada-hadan kudade a cikin kasuwan cinji da sauran hanyoyi da suke samun kudaden shiga. Kwamitin ya kara jaddada cewa, za su ci gaba da bayar da hankalin su ga hada-hadar kasuwancin kasashen ketare,kamar yadda suka gudanar hkarkokin kasuwanci a ranar 19 ga watan Nuwambar shekarar 2020 wanda aka sami ba dala biliyan  35.18, idan aka kwatanta da na watan Satumbar shekarar 2020 wanda aka samu dala biliyan 35.95, a dai-dai lokacin da ake kara samun karuwar farashin danyan mai a kasuwar duniya.

SendShareTweetShare
Previous Post

Ranar Ciwon Hakarkari Ta Duniya

Next Post

Gwamnatin Tarayya Ta Bude Sabon Shafin Dubarun Farfado Da Tattalin Arziki – Osinbajo

RelatedPosts

Lantarki

Bangaren Lantarki Ya Tafka Asarar Naira Biliyan 20.5 Saboda Karancin Gas

by Muhammad
22 hours ago
0

Bangaren wutar lantarki a Nijeriya ya tafka asarar harajin naira...

Matsalolin

Masana Sun Bayyana Hanyoyin Da Nijeriya Za Ta Bi Wajen Dakile Matsalolin Tattalin Arziki

by Muhammad
23 hours ago
0

Masana harkokin kudade da na tattalin arziki sun bukaci gwamnati...

Tattalin arziki

Yadda Ta’addanci Ya Lakume Tattalin Arzikin Dala Miliyan 80 A Arewa – Buhari

by Muhammad
23 hours ago
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta...

Next Post
Farfado

Gwamnatin Tarayya Ta Bude Sabon Shafin Dubarun Farfado Da Tattalin Arziki – Osinbajo

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version