Nijeriya za ta karɓi bakuncin gasar karatun Alƙur’ani ta kasa da kasa a watan Agustan bana. Taron, wanda zai samu halartar wakilai daga ƙasashe kusan 20, yana gudana ne ƙarƙashin jagorancin tsohon ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Bassa/Jos North a Jihar Filato, Muhammad Adam Alkali.
A wata sanarwa da aka fitar wa ‘yan jarida a ranar Alhamis, an bayyana cewa gasar za ta fara ne a birnin Jos, babban birnin Jihar Filato, yayin da za a kammala ta a Abuja.
- Atiku Zai Bude Kwalejin Mahaddata Al-Qur’ani Mai Cin Dalibai 500 A Ziyarar Da Zai Kai Kano
- Kwastam Ta Kama Jirage Marasa Matuka Da Sauran Kayayyaki Da Darajarsu Ta Haura Naira Biliyan 921 A Legas
Alkali ya nuna godiyarsa ga Cibiyar Nazarin Musulunci ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto (UDUS) saboda tallafi mai ƙarfi da ta bayar, yana mai jaddada cewa Alƙur’ani mai girma shi ne ginshiƙin rayuwa mai ma’ana ga musulmi da ke neman shiriya.
Shugaban kwamitin shirye-shirye, Gwani Sadiq Zamfara, ya bayyana ci gaban da aka samu a fannin shirye-shiryen taron, yana mai tabbatar da cewa komai yana tafiya daidai don ganin an gudanar da gasar cikin nasara, idan babu sauyi aka samu ba.
Wannan gasar za ta haɗa wakilai maza da mata daga ƙasashe kamar su: Kamaru, da Ghana, da Chadi, Senegal, da Kenya, da Tanzaniya, da Mauritania, da Nijar, da Masar, da Moroko, da Libya, da Aljeriya, da Saudiyya, da Kuwait, da Qatar, da Malaysia, da Ingila, da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), da Amurka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp