Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) Reshen Jihar Bayelsa ta horas da jami’anta a kan hanyoyin da za su inganta basirarsu musamman a kan hanyoyin kyautata rayuwarsu.
Hukumar, reshen jihar ta gayyato Kamfanin da ke bunƙasa ƙwazon ma’aikata, TINBIRD NIGERIA LIMITED domin ya horas da jami’an musamman kan abin da ta yi wa taken “Me ya kamata a yi bayan ritaya”.
Horaswar ta fi mayar da hankali ce a kan yadda jami’an za su fahimci alfanun sana’o’i kamar noman rogo, kiwon zomo, kiwon dodon koɗi da sauran dabbobin da ake ci na rayuwa da aka fi amfani da su a Jihar Bayelsa.
An ƙarfafa gwiwar jami’an su riƙa gudanar da rayuwarsu daidai da abin da suke samu a matsayinsu na masu albashi, amma su ƙarfafa abokan aurensu su rungumi sana’o’i.
Ƙwararriyar mai horaswa a taron, wacce har ila yau ta gwanance wajen iya jawabi a bainar jama’a a Nijeriya da Amurka, Abigail Bokoyeibo, ta faɗakar da jami’an a kan muhimmancin kula da ƙa’idojin aiki da ririta wani abu daga cikin albashinsu tare da zuba jari a sana’o’in da za su kyautata yanayin rayuwarsu tun suna bakin aiki.
Ta kuma nuna wa jami’an muhimmancin ƙarfafa iyalansu musamman waɗanda suke zaune ba su aikin komai, ta hanyar tsunduma su a sana’o’in gyaran gashi, aski, ado da kwalliya da ɗinki, sayar da ruwan burtsatse, sana’ar shige da ficen kuɗi ta POS baya ga noma da aka yarda wa kowane ma’aikacin gwamnati ya yi.
Daga cikin ƙwararrun da suka halarci horaswar har ila yau akwai Jami’ar Bunƙasa Kasuwanci ta Makarantar Tibird, Sarauniya Sese Ayoro, da Hon. Bibian George ta Cibiyar Bunƙasa Ci Gaban Mata da sauransu.
Da yake jawabi a taron horaswar, Kwanturolan NIS na Jihar Bayelsa, CI Sunday James ya nanata wa jami’an muhimmancin aiki tare da shawartarsu su ɗauki horaswar da muhimmanci tare da aiki da abin da aka horas da su a kai.
A cewar James, shekara 35 ta ritaya daga aiki kamar sanarwa ce ga duk ma’aikaci a kan ya shirya wa ritaya daga ranar da ya fara aiki.
Ya ba da misali da wani zancen hikima da masani Collins Powel ya yi a littafinsa mai sunan “Ranar Ritaya ta ƙarshe”, inda ya jaddada cewa ranar ritaya ta ƙarshe ita ce ranar tattara komatsai a yi sallama da kuma tafiya gida da abin da ka ririta lokacin da kake aiki, sai katin shaida.
Wakazalika, Kwanturolan ya ƙarfafa gwiwar jami’an hukumar su ɗauki ayyukansu da muhimmanci tare da kauce wa tserewa a bakin aiki ba tare da izini ba saboda gudun rasa aiki, domin ga masu neman aiki nan birjik suna gararamba a kan titi, don haka akwai buƙatar su ƙara riƙe abin da ke hannunsu da kyau.
Kwanturolan ya yi godiya ga Shugaban Hukumar ta NIS, muƙaddashin CGI Isah Idris Jere bisa ba su damar nuna ƙwarewarsu ta shugabanci a manyan ressan hukumar.
Horas da jami’an dai za ta ƙara musu ƙwazon aiki da kyautata jin daɗin rayuwarsu.