Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ta naɗa Queen Stephanie Chukwuemeka a matsayin jakadiyar fasfo domin ƙara bunƙasa ɓangaren fasfo da hukumar ke samarwa a jihar.
Kwanturolan NIS reshen Jihar Ribas, CIS Sunday James ya sanar da haka ga manema labarai, inda ya ƙara da cewa hukumar ta yi la’akari da nasarar da Queen Stephanie ta samu a rayuwa da kuma yadda hakan zai ƙara wayar da kan jama’a game da harkokin fasfo a jihar.
Har ila yau, James ya bayyana cewa naɗin Queen Stephanie da NIS reshen Ribas ta yi, wani yunƙuri ne na nuna goyon bayan hukumar ga ɓangaren fasahar ƙirƙira da nishadantarwa.
“Ita Queen Stephanie ta sanya Nijeriya alfahari a tsakanin ƙasashe sakamakon lashe gasar da aka yi ta Sarauniyar Afirka ta ‘Yan Mata ta shekarar 2023, wadda aka gudanar a Accra, ƙasar Ghana a ranar 26 ga Agustan 2023.” In ji James.