Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS), ta kaddamar da sabon tsarin tsaurara tsaron iyakoki a jihohin Arewa Maso Gabas da suka hada da; Adamawa da Bauchi da Borno da Gombe da Yobe da kuma Filato.
Wannan matakin, na zuwa ne karkashin jagorancin Kwamptrola Janar na hukumar, Kemi-Nanna Nandap, wadda ta ce an yi hakan ne domin kara tsaurara tsaron iyakoki saboda karuwa na matsalolin tsaro.
- Gwamnonin Nijeriya Sun Aminta Da Salon Mulkin Tinubu
- Gwamnati Ta Fara Tattaunawa Da ‘Yan Kasuwa Don Karya Farashin Kayan Abinci A Nijeriya
Sabon tsarin zai gudana ne karkashin jagorancin ACG James Sunday, wanda aka umarci shugabannin NIS na yankin Shiyya ta C, da su kara kaimi wajen sintiri da hada kai da sauran hukumomi domin hana shige da ficen ba bisa ka’ida ba.
Aikin zai mayar da hankali kan hana shigowar wadanda ba su da izini da tabbatar da tsaron iyakoki yadda ya kamata.
NIS, ta tabbatar da cewa za ta kula tare da sanya ido wajen kula da masu izinin shigowa cikin kwarewa da mutunta doka.
Hukumar ta ce kuma za ta jajirce wajen kare iyakokin kasar nan ta hanyar aiwatar da dokar Shige da Fice ta 2015 da kuma mayar da duk wanda aka samu ba bisa ka’ida ba zuwa kasarsa.