Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Kamfanin NNPC ya yanke hukunci rufe matatun man fetur guda uku a Nijeriya sakamakon gudanar da wasu ‘yan gyare–gyare na wucin gadi wanda hakan zai ba su damar yin cikakken aiki yadda ake bukata.
Babban Daraktan NNPC, Dakta Maikanti Baru ne ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki game da sha’anin bututun mai da Kungiyar Kula Da Bututun Man Fetur suka shirya a Abuja wanda kuma an shirya taron ne da nufin dawo da martabar matatun man fetur na Nijeriya.
Dakta Buru ya ce gyaran fuskar zai shafi matatun man fetur da ke Warri da Kaduna da kuma na Fatakwal, wanda yanzu haka suke aiki kasa da kaso 30 cikin 100 na adadin da ake bukata, a cewarsa, garambawul din zai bawa matatun damar gudanar da aiki yadda ya kamata, wanda ake son kammalawa daga nan zuwa 2019. Matatun dai ana sa ran za su canja yanayin aikin da suke yi na samar da ganga 650,000 a kowace rana. Ya ce fatan da ake yi shi ne, matatun guda uku su fara aiki kafada da kafada da matar mai ta Kamfanin Dangote, wadda ake sa ran za a bude ta a 2019.
Shugaban ya cigaba da cewa, “akwai kyakkawan fatan cewa matatun man za dawo aikin tare da kayayykin aiki na zamani, wanda zai taimawa Nijeriya ta rage shigowa da mai daga kasashen waje kafin nan da shekara ta 2019.”
Har ila yau ya maida martani ga wasu ‘yan Nijeiya da suke da tunanin cewa ba za a taba gyara matatun man fetur ba har abada, ya kara da cewa a wannan karon an shirya tsaf domin fuskantar gyaran su.
Dakta Maikanti ya bada tabbacin cewa matatun man za su dawo da karfinsu kuma sabbi fil domin cigaba da aikin tace mai, duk da cewa wannan abu da zai kawo cikas amma kafin a kammala aiki.
A wani labarin kuma, Shugaban Rukunin Kamfanin mai na NNPC Dakta Maikanti Baru ya kaddamar da kwamiti na mutun takwas da zai jagoranci dawo da martabar matatun man fetu sannan a tabbatar suna aikin kamar yadda ake bukata kafin zuwa shekarar 2019.
Wannan yana kunshe ne a cikin wata takarda da kamfanin NNPC ya rabawa manema labarai a Abuja, inda ya ce wannan yana daga cikin kudirorin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na gyara matatun man fetur guda uku.
Jim kadan bayan kaddamar da kwamitin, Dakta Maikanti Baru ya ja hankalin membobin kwamitin da su fidda san rai wajan tafiyar da wannan muhimmin aiki domin a tabbatar matatun man sun dawo da maratbarsu da aka san su da ita tun asali.
Ya kara da cewa, “na tabbatar wannan tawagar an zabe ta domin yin wannan
Dakta Maikanti Baru ya ce a lokacin gudanar da wannan aikin ana sa ran
kwamitin zai yi iyakar kokarainsa na ganin an kammala aikin ciki sauri ba tare da tsaiko ba.