Jam’iyyar NNPP ta zargi gwamnatin jihar Kano da kai hare-hare kan mutanen da ba su ji ba su gani ba bayan ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna na 2023 da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi.
Jam’iyyar a cikin wata sanarwa da ta fito daga shugabanta na jihar, Hon Umar Haruna Doguwa, ta ce wasu ‘yan daba da ake zargin gwamnatin jihar ce ta dauki nauyinsu sun ba da umarnin kai hare-hare a wurare daban-daban a cikin birnin jihar.
Sanarwar ta ce jam’iyyar NNPP ta nuna takaicinta kan salon APC na yadda take nuna damuwarta kan rashin nasarar lashe zaben gwamna a 2023.
“Mutanen Kano za su iya tuna cewa bayan ‘yan mintoci kadan da bayyana nasararmu mai dimbin tarihi, zababben gwamnan NNPP Abba Kabir Yusuf ta bakin mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar da sanarwa inda ya bukaci daukacin magoya bayansa da su gudanar da murnarsu cikin lumana a yayin bukukuwan nasarar jam’iyyar, yayin da ni kaina a matsayina na shugaban NNPP na jihar na kasance a gidajen rediyo daban-daban ina kara kira kan hakan, kuma magoya bayanmu sun bi umarninmu amma ‘yan daban jam’iyyar adawa sun fara kai hare-hare ga mutanenmu.
“Jam’iyyar NNPP tana da sahihan bayanai cewa, gwamnatin jihar na sake shirya wani tashin hankali da sunan zanga-zangar adawa da INEC da jami’an tsaro da ke aiki a Kano kan rashin nasarar APC a zaben gwamna da aka kammala.
“A halin yanzu mun samu labarin ana tattara motoci 50 na ‘yan daba daga kowace karamar hukuma 44 da nufin lalata dukiyoyin jama’a da cibiyoyin INEC a fadin jihar. Shirin shi ne a yi amfani da jar hular Kwankwasiyya wajen aikata wannan mummunan aikin.”