Connect with us

NOMA

Noma Tushen Arziki: Dabarun Noman Doya

Published

on

Tare da Yahaya Usman Alfadarai 07084634387 09096984945

NAERLS/ABU ZARIA Samaru Zariya

  • Zaben Wuri (Gona)

A zabi wuri mai dausayi wanda ya ji taki sosai, ko kuma kana iya noma ta a gonar da ka noma masara ko dawa, ko wuri mai kama da fadama wanda ruwa bai kwantawa malemale ya dade a ciki. Idan kuma da hali, akan so a rika canjin wurin shuka a kowacce shekara.

 

Gyaran wuri da yin shuka:

  1. Yi sabce ka shirya manyan kunyoyi ko bunga da zarar ka gama girbin gyero ko kuma ruwan sama ya dauke dungun.
  2. Girman kunyar ko bungar da za ka yi ya danganta ga irin doyar da za ka shuka, amma dai ana bukatar yin mayan kunyoyi.

Misali idan doyar nan kanana sirara za ka shuka, to sai ka shirya bungar masu nisan tsakanin kafa hurhudu da bisan kafa ko kafa uku (4×4ft) ko (4×3ft).

Idan ka zo yin shukar sai ka yi da lura kamar yadda ka saba. Wato za ka dan sara bisan kunyar ka sanya doyar a kwance, ka binne, daga nan sai ka tsakuri taki kadan ka binne kusa da tushen doyar, misalin nisan inci 3-6 sa’annan sai ka debo karan gyero ko na masara ko ciyawa ka rufe kan kunyar, maganin zafin rana. Wannan shine ake ce da shi malein kuma ya kan taimaka sosai wajen rage rubar doya.

Lokacin shuka doya

A kan shuka doya misalin sau biyu a shekara. Ta farko ita ce wadda ake shukawa da kaka wato da zarar an gama yin balla, misali cikin watan Oktoba zuwa Nuwamba – shukanta biyun kuma akan yi ne lokacin bazara, wato daga watan Fabrairu zuwa Afrilu, ko har zuwa faduwar damina.

 

Zaben Iri:

Akwai doya iri-iri da akan shuka a wurare daban-daban. Misali akwai wadda ake kira Ashola, da Ashamula da Arimu da Aduru da Atalube da Amara da Akoki da Gwari da Dan Amarya da Dan Dio, da Cikawa da ‘Yar Igabi da dai sauransu birjik.  Amma domin mai karatu ya gane za mu raba doyar kashi hudu. Wato farar doya da rawaya (marar nuna da wuri), da doyar ruwa da doyar danga da doya mai ganye uku. Yana da wuya a nan mu bugi kirji mu ce ga irin doyar da ya fi dacewa a shuka a kowanne lungu na kasar nan. Dan haka sai ka shuka irin wadda ta fi yin kyau a karkarar ku.

Idan an zo zaben irin, an fi son a zabi cikakkiyar saiwa a shuka. Amma idan hakan zai wahalar – akan iya yanka babbar saiwa kashi uku- wato ka da tsakiya da gindin a shuka kowannensu. To amma sai a lura za a yanka irin ne misalin kwana daya ko kwana biyu kafin shukar. Yin haka yakan sa bakin yankan ya bushe, kuma yakan taimaka wajen rage rubar doyar, kan ya fi gindin da tsakiyar, haka kuma gindin ya fi ysakiyar bada iri mai kyau.

 

Maganin Buzuzu

Akan yi amfani da Aldrin Dust  Gamalin ‘A’ shi wannan maganj garin hoda ne kuma yawanci manoma sun san shi.

Ga kowanne pakiti daya akan iya cude tushe 120 na irin doya. Yadda za ka yi shine, sai ka zazzage pakiti daya cikin daro ko kwarya. Daga nan sai ka juye irin a hankali ka dasa. Amma yawancin manoma sukan cude maganin ne da yashi ko tubaya sa’annan sai su rika dosana hancin doyar musamman wajen da aka yanka, daga nan sai a yi shukar yadda aka saba. To ko ma dai wace hanya ka bi akan yi wannan ne dan maganin buzuzu da sauran kwari da tsutsotsi masu lalata doya.

 

A lura:

Ba a cin irin wannan doya da aka sa mata magani, domin maganin dafi ne.

 

Takin zamani:

Doya kamar dai sauran shuke-shuke tana bukatar taki, kuma an lura ta fi son taki dangin mai gishiri – wato takin yuriya, ko ‘Superphosphate’. Amma kuma manoman kasan nan sukan kara da ‘Super’ da Kampa. Idan yuriya aka samu masu nauyin buhu daya da rabi masu nauyin kilo hamsin ya wadatar ga kowacce hekta. Idan kuma ‘Superphosphate’ aka samu to buhuna biyu da rabi masu nauyin kilo hamsin sun isa ga kowacce hekta.

A kan zuba takin ne ta hanyar ga naka bayan misalin wata biyu da yin shuka ko kuma bayan an ga fiye da rabin dashen sun fara sabon toho.

Amma manoma sukan zuba ‘Superphosphate’ ne da zaran sun yi shuka, daga nan suna iya kara kamfa ko uriya daga baya. Ga yadda za ka zuba takin:

  1. Za ka tsakuri taki ne, ka yiwa dashen barbade da nisan da’irar tsakani da gindin tushe misalin inci 6 zurfin ramin da za a zuba kuma kada ya gaza ‘inci 2’ daga nan sai a sa kasa a rufe.
  2. Ko kuma ka toni rami mai dan zurfi a kusa da kowacce shuka sa’annan ka tsakuro takin ka zuba ka binne- domin kada ruwa ya wanke takin a yi hasararsa.

 

Ratayar Kurinyara Doya

Wannan wata hikima ce da manoman doya kan yi domin inganta noman doyarsu, wato don samun isasshen hasken rana ga itacen doyar, gwanayen noman doya sukan bi kowanne tushe ne su kakkafa itatuwa ko karan dawa ko masara su rataye kurinyar doyar. Yin haka yakan taimaka wajen bunkasa saiwar doya.

 

Hadaka A Gona

An fi so a shuka doya ita kadai a gona, amma yanzu manoman doya sukan yi hadakarta da sauran shuke-shuke kamar su barkono ko attarugu da kubewa da masara ko dawa, a wadansu wuraren ma har ‘Guna’ akan shuka cikin gonar doya. Manoma kan kira wadannan shuke-shuke hanjin gona.

To amma a halin gasikiya yin wannan hadakar tana da tata illar. Misali idan aka shuka ‘Guna’ cikin gonar doya, yawan doyar da za a samu yakan iya raguwa har da kashi tamanin a cikin dari. Haka nan kuma idan aka shuka masara akan yi hasarar doya fiye da rabi, kuma yawan masarar da za a samu yakan ragu da kusan kashi 30 cikin dari.

 

Yin Noma:

Yi noma ka tada kunya a duk lokacin da ya dace. Kuma musamman akan so a yaye karan masara ko busasshiyar ciyawar nan da aka rufe duk wata saiwa da ta fito waje da kasa. Saboda a saukake wahalar fama da ciyawa, masu bincike wato (Research) sun dukufa don gano wane irin maganin kashe ciyawa ne ya fi kamata a zuba a gonar doya.

 

Ginar Doya:

Kafin doya ta kosa ta isa gina (tono) akwai wani abu da akan yi mata wai shi BALLA, kuma musamman akan yi wannan balla ne cikin watan Yuni zuwa watan Agusta.

 

Ga Yadda Akan Yi Balla

Za ka dan samo itace ne mai dan tsini, kamar fegi ka tona saiwar doyar a hankali. Daga nan sai ka karye – wato ka ballo misalin rabin ko daya bisa uku na wannan saiwar, ka bar sauran a jikin tushen doyar ka maida kasa ka binne, wannan zai sa doyar ta yi kwaya ta kuma bada iri da amfani mai yawa. To wannan hukuma ita ce ake kira ‘Balla’. Bayan misalin wata daya zuwa biyu da yin Balla, doyar ta isa gina kenan, don haka akan iya fara ginar doya tun daga Oktoba har zuwa watan Janairu.

Alamomin da za su nuna doya ta isa gina shi ne, za ka ga ganyenta ya fara bushewa suna kakkabewa. To da ganin haka idan har lokacin gina ne, to sai ka nemo magirbi ko fartanya ko kuma diga, ka ci gaba da ginar doyarka. Amma kuma a kan so a yi da kula domin kada a karya kwayar, ko kuma a yi mata rauni.

 

Ajiyar Doya:

Akwai hanyoyin ajiyar doya daban-daban muhimmai daga cikinsu su ne:

  1. Ajiye ta yin amfani da dogayen itatuwa: Za a kafa dogayen itatuwa ne cikin inuwa layi bibbiyu, daga sai sai a bi ana daure doyar guda guda ana jerawa jikin wadannan dogayen itatuwa. Ta wannan hanyar akan iya ajiye misalin ton guda na doya ta yin amfani da itatuwa guda 76.
  2. A kan ajiye doyar a daki mai sanyi: Misali daki mai rufin jinka ko silin ko kuma kana iya ajiye ta cikin inuwa ka rufe da ciyawa. Abin lura dai anan shine ba a so a bar doyar a waje cikin zafin rana. Yin hakan ya kan sa ta bushe ta farfashe, daga nan kuma sai ta rube ta lalace. Saboda haka idan aka yi ajiyar doyar wajibi ne a rika bi ana fidda duk wadda ta rube ko ta kamu da wani ciwo. Domin barinsu cikin doya mai lafiya yana da illa ainun.
  3. Wata hanyar ajiyar doyar da mutane kan bi itace ta yin ajiya cikin rami, wato akan toni rami ne mai zurfi, daga nan sai ka yi ta shimfida ciyawar, wato haka dai za yi ta yi kana shimfida ciyawa kana shirya doya bisanta har ramin ya cika sa’annan sai a rufe da ciyawa.

Fadakarwa:

Don samun ribar noman ka:

– Zabi wuri mai kyau

– Gyaran wurin sosai a cikin lokaci

– Zabi iri mai kyau ka shuka da wuri

– Ka kula da sa taki da yin melcin

– Ka kula da yin noma da yin sitekin

– Yi gina cikin lokaci kuma ka yi

– Kyakkyawar ajiya.
Advertisement

labarai