An shafe sama da shekaru da yawa a Nijeriya ana samun riba mai yawa jarin da ake zuba jari noman Kashu, haka kuma kwallon kashu, ana fitar da shi zuwa kasuwar duniya don sarrafa shi zuwa wasu nau’ukan amfani.
‘Ya’yan bishiyar kashu na fara yi ne daga wata uku zuwa hudu kuma noma ne da ake zuba jari na dogon zango, haka kuma ana samun dibin riba, musaman idana aka fitar da shi zuwa kasuwar duniya.
Gyaran Gona:
Ana bukatar wanda zai fara noman kashu, ya tabbatar gonarsa ce ba ta haya ba, musamman ganin cewa, fanni ne na dogon zango.
Ana kuma samun mai daga jikin Kashu da wasu kamfanoni ke sarrafa shi zuwa wasu nau’uka.
Lokacin Da Ya Fi Dacewa Manoma Su Shuka Kashu
Shuka Kashu na da matukarar wahala, kusan daidai da yadda ake noma kwakwar manja da kuma yadda ake shuka kwarar Kofi, inda a saboda haka ne, ake bukatar wanda zai fara nomansa, ya tabbatar da ya samo inganataccen iri.
Irin nasa na kai wa tsawon shekara uku kafin a fara dibansa.
Zuba Takin Zamani:
Kashu na bukatar a zuba masa takin zamanin da ke dauke da sinadarin Nitrogen da Phosphorus da kuma Zinc, domin wadanan sanadaran, na taimaka masa matuka, wajen saurin girma.
Yi Masa Ban-ruwa:
Ana son a yi masa ban-ruwa da lokacin rani ko kuma a lokacin da fari ke fara kunno kai, domin wadannna lokutan ne, da ya fi bukatar ruwa.
A lokacin damina kuwa, ba a ba shi, sai dai wanda yake nomansa ya bai wa kansa wahalar ban-ruwa ba, amma a lokacin rani, ana son ka ba shi ruwa a sati sau daya ko kuma sau biyu.
Yi Masa Feshi Don Kare Shi Daga Cututtuka:
Wasu cututtua na harbin saiwoyinsa, don magance hakan, ana son ka yi masa feshi.
Lokacin Yin Fara Dibansa:
Kashun na fara nuna ne daga farkon watan Janairu haka ana son lokacin da bishiyarsa ta fara zubo da su kasa, ana son ka tabbatar da kana dibansa.
Ana kuma son ka cire ciyawar da ke ke gindin bishiyarsa, yadda za ka ji saukin kwashe shi, inda kuma bushewar kwallonsa na kai wa tsawon kwana biyu zuwa uku.
Yadda Ake Adana Kwallon Kashu:
Ana son ka adana kwallonsa a cikin buhu don kare shi daga lalace wa.
Haka ana son ka ajiye buhun a kan wani katako, ba a kuma son ka aji ye shi a gurin da ke da lema don ka da ya lalace.
Hada-hadar Kasuwancinsa:
Ana son kafin wanda ya shuka Kashu ya fara dibansa, ya tuntubi kamfanonin da suke da bukatarsa, musamman don kai shi kasuwannin duniya.
Idan kuma ba ka son bin wannan hanyar, kana iya tallansa a kafar sadarwa, musamman don manyan kamfanoni da ke sarrafa shi zuwa wasu nau’uka daban-daban.
Masu iya magana na cewa, Barewa ba za ta yi gudu ba darta ya yi rarrafe ba, inda kuma noman kashun ke taimaka wa wajen kara sama riba.
Ana Samun Kudi Mai Yawa Daga Kiwon Barewa
A kalla, ana sayar da barewa daga naira 130,000 zuwa naira 200,000, amma ana bayar da shawara cewa, dukkan wanda ke son kiwata barewa ya saye ta tun daga lokacin da aka yi bayenta wato daga wata takwas.