NYSC Za Ta Dauki Mataki Kan Jami’an Dake Taimakawa Wurin Saba Ka’ida

Hukumar NYSC ta jihar Legas ta ce zata dauki mataki a kan duk wata ma’aikata da ta daure wa ‘yan yi wa kasa hidima gindi wajen kin zuwa wajen aiki a yayin aikinsu na bautawa kasa.

Shugaban hukumar na jihar Legas Mista Mohammed Momoh, ya bayyana haka a bukin rufe horawar da ya gudana na ‘yan bautan kasa na “Batch ‘B’ Stream II” a sansanin ‘yan bautan kasa da ke Iyana-Ipaja a Legas.

Momoh ya kuma bukaci ‘yan bautan kasan su yi biyyya ga dokoki da ka’idojin hukumar saboda duk wanda aka samu ya saba za a hukunta shi daida da dokokin hukumar.

Ya ce, wasu hukumomi kan hada kai da masu yi wa kasa hidima wajen karya dokokin hukumar.

“Mun sanar dasu cewa, wannan halin ba shi da kyau kuma bai kamata ba, wadannan matasa ne aka basu amana da nufin su ba su horan da ya kamata”

“Yayin da ka bar mai yi wa kasa hidima ya bar wurin aiki ba tare da cikakken izini ba, hakan ba zai taimaki hukumar NYSC da ma ci gaban tarayyar Nijeriya ba”

“Mun gargadi da yawa daga cikinsu amma duk wanda muka kama da wannan laifin zamu sanya masa takunkumi, zamu daina tura masa ‘yan bautan kasa”

Momoh ya kara da cewa, an horar da ‘yan bautan kasan da horo na musamman a fannin rawar sojoji da gudanar da sana’o’i da yadda zasu gudanar da shugabancin al’umma a dukkan in da suka samu kansu.

“Ina sanar da ku cewa, Nijeriya na alfahari daku, ana sa ran zaku yi amfani da horan da kuka samu wajen taimaka wa alumman da zaku yi aiki dasu”

Shugaban na jihar ya kuma bukaci ‘yan bautan kasar su yi aiki tsakaninsu da Allah a duk inda suka samu kansu

A nasa jawabin, gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambode, ya bukaci ‘yan bautan kasan dasu yi aiki tukuru a yayin da suke gudanar da aiyukansu na taimakon alumma, kwamishinan aiyyuka na musamman a jihar Mista Olusrye Oladejo ne ya wakilce shi, ya kuma kara da cewa, “Sirrin aiki tukuru shi ne nuna soyayya akan abin da kake yi ko da kuwa ba za a biya ka ba, wannan sirrin shi ne ke zama ginshikin ci gaba a harkokin rayuwar mutum” an karrama mutum 6 da lamba na musamman saboda kokari da jajircewansu a lokacin horaswar na mako 3.

 

Exit mobile version