Bello Hamza" />

Obasanjo Kasurgumin Dan Magudin Zabe Ne –Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kwatanta tsohon shugaban kasar nan Cif Olusegun Obasanjo da cewa, shi wani shaharraren dan magudin zabe ne mai hana kansa hutu, tun da har ya iya cewar, kada shugaba Muhammadu Buhari ya sake neman wa’adi na biyu a zaben shekarar 2019.
Amma a nasa martanin, wani hadimin shugaba Obasanjo, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce, wannan magana abin takaici ne kwarai da gaske musamman ganin maganan ta fito daga mutanen da suka nemi taimakon tsohon shugaban kasar a shekarar 2015.
“Wadannan fa su ne suka zo wurin wannan mutumin (Obasanjo) shekara 3 da suka wuce suna mai neman agajinsa a kan zaben 2015. Lallai mutane na sane faruwa wannan lamarin. Sai ga shi a halin yanzu kuma ace ya yi shiru kada ya bayyana ra’ayinsa. Wadannan mutanen har da Tinubu da kansa sun je wurin Obasanjo neman taimako, ba shi ya je wurinsu ba, yanzu obasanjo na cewa ne, abubuwa basa tafiya yadda ya kamata kuma Buhari ba zai iya tafi da mulki yadda ya kamata ba” inji Hadimin Obasanjo.
A jiya ne Tinubu ya yi wannan maganan a karshen babban taron jam’iyyar APC ta kasa a Abuja, inda ya kara da cewa, “wani mutum da yake tsohon janar na soja ne an kuma zabe sa a matsayin shugaban kasar nan, ina kiransa da sunan shaharraren mai magudin zabe, wai har yana da wani mutuncin da zai ce kada shugaba Buhari ya sake tsayawa takara,a wata jam’iyyar? Alhamdulilahi tunda ba a jam’iyyarmu ta APC yake ba.”

Exit mobile version