Tsohon dan takarar Shugaban kasa a karkashin jam’iyya Labour Party, Mista Peter Obi, ya yi alkawarin zai biya kudin jarabawar (NECO) na fursunoni 148 wadanda suke zaune a gidajen gyara halin ka a sassa daban daban na Jihar Anambra.
Obi ya bayyana hakan ne bayan da ya gana da wakilan su fursunoni daga Awka, Onitsha, Nnewi da kuma Aguata na Jihar Anambra.
- Babu Ɗalibin Da Aka Sace A Makarantar St. Peter’s A Nasarawa – ‘Yansanda
- 2027: Ganduje Ya Gargaɗi Mambobin APC Kan Fara Tallata Masu Neman Takarar Gwamna Da Wuri
Fursunoni wadanda suke rubuta jarabawa NECO, na iya shiga matsala saboda rashin biyan kudaden jarabawar.
Kamar yadda bayanin alkalumma suka nuna wadanda aka kai ma Obi, Awka na da 50, Onitsha 36, Nnewi 25 da kuma Aguata 37, gaba daya fursunoni 148 ke nan.
Kowane dalibi zai biya ₦aira 30,050 a matsayin kudin jarabawa da kuma karin ₦aira 2,000 saboda wani abu daban, hakan yasa kudaden suka kasance Naira 32,050, gaba daya sun kai jimillar ₦aira milyan 4,741.400.
Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya ba tawagar wakilan tabbacin cewar zai biya kudaden domin tabbatar da an barsu sun gama rubuta jarabawa ba tare da kawo masu wata matsala ba.
Ya ce zai yi aiki tare da masu ra’aytinsa da kuma magoya bayansa domin a samu dama ta tara kudaden da ake bukata.
“Zan rubuta ma wakilan ranar Litinin domin tabbatar da cewa za’a iya biyan kudin, wanda hakan zai sa fursunonin su ci gaba da rubuta jarabawa.
Tsohon gwamnan ya kara jaddada cewa ilimi ya kasance wani babban abu ne na gyara al’amura masu yawa, ya ce wuraren ko gidajen gyara halinka wasu wurare ne da ake gyara halayen masu laifi ba wai su kasance wuraren da za a rika azabtar da suu ba.Obi,wanda ba da dadewa bane ya kai ziyararar Jami’ar Jihar California, Sacramento, kan wadansu tsare tsare da suka hada da lamarin daya shafi bada shawara kan lamarin karatu da kuma wadanda suke tsare sanadiyar wani laifin da suka aikata, da kuma wasu daidaikun mutane.
Ya nuna rashin jin dadinsa akan yadda ba a bayar da dama ta samun ilimi ga wadanda suke gidan gyara halinka a sassa daban daban na kasa, inda yace ai rashin samun ingantaccen ilimin ne yake sa irin wadanda suke cikin halin aikata laifin da suka dama.
“Idan mutane suka kammala wa’adin gidajen gyara halinka, dole ne su kasance sun samu mallakar abubuwan da za su sa su taimakawa al’umma, da kuma sake sa kansu hanya madaidaiciya domin jin dadin rayuwarsu.
Shugaban Kasa Tinubu Ya Amince Da Kafa Shugabannin Hukumar Kula Da Jami’oi Karo Na 13
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da nada Shugabannin Hukumar kula da Jami’oi ta kasa a karo na 13 (NUC), inda ya amince da Emeritus Farfesa Oluremi Raphael Aina, OFR ,a matsayin Shugaba .
Shugabannin Hukumar da ba’a dade da kaddamarwa ba, a ma’aikatar ilimi ta tarayya tare da Shugabannin hukumar binciken harkokin ilimi, da ci gaba (NERDC), Cibiyar harkokin Malamai ta kasa (NTI), da kuma hukumar ilimin bai daya (UBEC).
A na shi bayanin, Ministan ilimi, Dakta Tunji Maruf Alausa, ya bayyana cewa Shugaban kasa yayi matukar amincewa da su Shugabannin wajen bayar da shawarar data kamata saboda kwarewar da suke da ita,ilimin da suke da shi wajen yiwa Hukumar jagoranci yayin da shi bangaren ilimin yake aiki domin tabbatar da irin kudurin da gwamnatin tarayya take da shi a karkashin jagorancin Tinubu .
Ita ma hukumar kulawa da harkokin jami’oi ta yi maraba da sabbin Shugabannin nata inda ta yi fatan za su tafiyar da ayyukansu fiye da yadda kowa ya k e tsammani ta hanyar samar da nagarta, shigo da wasu abubuwa a fadin Jami; oin da suke illahirin kowane sako da lungu na Nijeriya.














