Ovie Omo-Agege Ne Ya Zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa

Sa’o’i Kadan da kammala zaben Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, inda Ahmad Lawal mai wakiltar Yobe ta arewa kuma dan jam’iyyar APC mai mulki, ya samu nasara akan abokin karawar shi, Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta kudu, shi ma dan jam’iyyar APC mai mulki.

An kada kuri’ar mataimakin Shugaban Majalisar ne tsakanin tsohon mataimakin Shugaban Majalisa Eke Ekweremadu na jam’iyyar PDP da kuma Ovie Omo-Agege na jam’iyyar APC mai mulki.

Omo-Agege ya samu nasarar zama mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan da gagarumin rinjaye, Omo-Agege mai shekaru 55 yana wakiltar mazabar Delta ta tsakiya ne a majalisar dattawan, an fara zabarshi ne a matsayin sanata a shekarar 2015, a karkashin inuwar jam’iyyar Labour, inda a a cikin shekarar 2017 ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Exit mobile version